Shirin 2023: APC ta sake jadawalinta, ta kara wa'adin sayar da foma-foman takara
- A karo na biyu, jam'iyyar APC ta sake dage wa'adin wasu shirye-shiryen ayyukanta gabanin babban zabe
- Jam'iyyar ta bayyana kara wa'adin sayar da foma-foman takara tare da fitar da sabon jadawalin jam'iyyar a jiya Laraba
- Wannan sauyi na zuwa ne daidai lokacin da wasu 'yan takara suka fara mika foma-fomansu wasu kuwa ke kara fitowa takara
Jam'iyyar APC ta sake tsawaita wa'adin sayar da fom din takara da sauran shagulgulan da ta sa a gaba gabanin babban zaben 2023.
Wannan sauyi na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka fara mayar da cikakkun foma-foman takara ga jam'iyyar a makon nan.
APC ta kara wa'adin sayar da fom din daga ranar 10 ga watan Mayu zuwa Alhamis, 12 ga watan Mayu, yayin da ta dage mayar da foma-fomai zuwa gobe Juma'a, 13 ga watan Mayu.
Wannan sauyin jadawalin dai shi ne na biyu a cikin makon nan, lamarin da ya bar wasu mabiya shafin jam'iyyar a Twitter baki-bude.
A wata takardar jerin abubuwan da jam'iyyar ta sa a gaba, wakilin Legit.ng Hausa ya ga sauye-sauyen da jam'iyyar ta samar, inda aka ga sauyin ya shafi dukkan lamurran da APC ta tsara ciki har da zabukan fidda gwani da ke tafe.
Sabon jadawalin zaben fidda gwani
Haka kuma an canza wasu ranakun zaben fidda gwanin sannan kuma sabon jadawalin ya kunshi ranaku kamar haka:
- Zaben fidda gwani na gwamnoni a ranar 20 ga Mayu
- Majalisun jihohi a ranar 22 ga Mayu
- Majalisar wakilai ta kasa a ranar 24 ga Mayu
- Majalisar dattawa a ranar 25 ga Mayu
Ga jerin sauran sauye-sauyen daga shafin jam'iyyar:
Tsohon Sakataren Gwamnati ya hango matsala, yace da yiwuwar a fasa zaben Shugaban kasa
A wani labarin, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Olu Falae ya na da ra’ayin cewa halin da ake ciki a Najeriya ya yi tabarbarewar da zai iya kawo cikas a 2023.
A wata hira ta musamman da aka yi da Cif Olu Falae a jaridar Punch, tsohon mai shekara 83 ya nuna cewa watakila zaben shekara mai zuwa ba zai yiwu ba.
Tsohon Ministan tattalin arzikin yake cewa a yadda ake tafiya, an fara hangen yiwuwar hakan. Falae yake cewa yanzu rayuwa ta zama babu tabbas, ana iya kashe mutum farat daya. Tsohon ya ce ba zai so ya zauna a Najeriya alhali ana wannan ta’adi ba.
Asali: Legit.ng