Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

  • Alamu masu karfi sun nuna cewa, hadimin shugaba Buhari ya shiga takara don haka ya ajiye aikinsa
  • Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Buhari ya umarni mukarrabansa da ke hangen kujerun siyasa a 2023 su ajiye aiki
  • An samu ministocin da tuni suka fara ajiye ayyukansu gabanin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC

Najeriya - Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya bayar ga mukarrabansa da ke neman takara cewa su gaggauta murabus.

Ahmad, wanda ya zabi shiga takarar dan majalisar wakilai a jam'iyyar APC, yana neman wakilcin Gaya, Ajingi da Albasu a majalisar wakilai ta tarayya.

Binciken da jaridar The Nation ta yi a yammacin Laraba ya nuna cewa Ahmad ya cire mukaminsa na mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai ga Buhari daga shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Bashir ya shiga takara, ya ajiye aiki
Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa | Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

A yanzu dai abin da yake jikin shafin nasa na nuni da cewa, shi yanzu ‘Digital Communication Enthusiast’ ne, kamar yadda Legit.ng Hausa ta bi ta tabbatar.

Ga sauyin da ya yi:

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa
Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ahmad dai zai kalubalanci dan takarar kujerar ne, Mahmoud Abdullahi Gaya, wanda kuma shi ma dan jam'iyyar APC mai mulki ne.

Ahmad dai shi ne wanda ake masa kallon daya daga cikin hadiman shugaba Buhari da ke da kananan shekaru, wanda aka nada yana da shekaru 24.

Kwanakin baya, ya yada wasu hotuna rike da foma-foman takara da ya saya na jam'iyyar APC mai mulki.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Yanzu na kammala cike fom dina, sauran kuma 'yan mazabata ne za su yi, mutanen kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a Kano, wadanda da yardar Allah zan wakilce su a majalisar wakilai. Allah (SWT) Ya ba mu NASARA!”

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Dan takarar shugaban kasa mai shekaru 35 ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

A gefe guda, wani dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Mista Ayoola Falola, a ranar Talata ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, yana neman soke tsarin zaben fidda gwani na jam’iyyar gabanin 2023 mai zuwa zabe.

Karar da ya shigar tana kalubalantar jam’iyyar ne kan kudin fom har N40m domin nuna sha’awa da tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Falola ya gama hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu a cikin karar da ya shigar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.