Bayan An Tara Masa N83m Don Siyan Fom Ɗin Takara, Adamu Garba Ya Fice Daga APC, Ya Bayyana Dalili
- Adamu Garba, tsohon matashin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar bayan an tara masa gudunmawa na N83m don siyan fom
- Garba ya bayyana cewa jam'iyyar ta kauce wa tsari na gari kuma ta fifita kudi a kan cancanta da kwarewa hakan yasa ta saka N100m kudin fom
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce a matsayinsa na wanda ya yi imani da Najeriya da fatan ganin cigabanta ba zai ya cigaba da zama a jam'iyyar da bata nufin kasar da alheri ba
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Adamu Garba ya sanar da murabus din sa daga jam'iyyar mai mulki a kasa.
Garba, wanda ya fice daga takarar shugaban kasa bayan masu gudunmawa sun tara masa N83m, ya soki jam'iyyar kan tsadan kudin fom din wato N100m.
Ya ce hakan wani yunkuri ne na yi wa matasa da sauran yan takara masu nagarta kora da hali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Garba ya ce ya yi niyyar siyan fom din takarar shugaban kasa na APC ne bayan ya tuntubi tawagar yakin neman zaben sa.
Amma, a ranar Laraba, ya wallafa rubuta a shafunkansa na sada zumunta, ya sanar da ficewarsa daga APC, yana mai cewa jam'iyyar ta kauce daga aƙidunta na alheri.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"Na rubuta wannan ne domin sanar da ka kai ficewa ta daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a hukumance.
"Na yi murabus ne domin yadda APC ta kauce daga hanyar alheri kuma ta dauki wasu matakai na ware wasu mutane wanda hakan ya saba wa demokradiyya.
"A matsayi na na matashi wanda ke fatan ganin cigaban Najeriya kuma ke yi wa APC kallon jam'iyya ta gari a baya, ba zan iya cigaba da zama mamba na jam'iyyar da ta fifita kudi da son kai a maimakon cancanta ba."
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng