Da duminsa: Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya yi murabus

Da duminsa: Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya yi murabus

  • Emeka Nwajuiba ya zama mutumin farko da yabi umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Nwajuiba, wanda shine mutumin farko da ya yanki Fom din takara na APC ya yi murabus daga kujerarsa na Minista
  • Buhari Ya Umurci masu niyyar takara kujerun siyasa umurnin su yi murabus daga kujerunsunan da kwanaki biyar

Abuja - Daya daga cikin Ministocin dake son gadon Shugaba Muhammadu Buhari kuma karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka yayi murabus daga kujerarsa.

Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya bayyana hakan a zaman majalisar zartaswar ya gudana ranar Laraba, rahoton DailyTrust.

Ya sanar da cewa Emeka Nwajuiba ya yi murabus daga kujerarsa ta Minista ne domin maida hankali kan yakin neman zaben zama shugaban kasa, riwayar Leadership.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Wannan ya biyo bayan umurnin da shugaban kasan ya baiwa masu niyyar takara kujerun siyasa umurnin su yi murabus daga kujerunsu da suke rike da su.

Taron FEC
Da duminsa: Karamin Ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, ya yi murabus Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari Ya Umurci Su Amaechi, Malami, Ngige Da Akpabio Su Yi Murabus Cikin Kwana 5

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.

Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari'a), Godswill Akpabio (Neja Delta).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng