Samun tikitin Jam’iyyar PDP ya fi karkata wajen Atiku, Gwamna Wike da wasu mutum 5

Samun tikitin Jam’iyyar PDP ya fi karkata wajen Atiku, Gwamna Wike da wasu mutum 5

  • A karshen watan Mayun 2022 ne za a san wanda zai rikewa jam’iyyar PDP tuta a zabe mai zuwa
  • Alamu na nuna samun tikitin jam’iyyar adawar ya fi karfi wajen wasu manyan ‘yan siyasa biyar
  • Atiku Abubakar, Nyesom Wike da kuma Peter Obi su na cikin wadanda ake ganin za a gwabza da su

A rahoton da ya fito daga Daily Trust a ranar Talatar nan, an yi bayanin yadda masu neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP su ke shiryawa zabe.

Jaridar ta ce alamu na kara nuna wanda zai rike tutar PDP bai wuce Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Peter Obi, Nyesom Wike ko kuma Aminu Tambuwal.

1. Atiku Abubakar

Shugabanni da jagororin jam’iyyar PDP a matakin BoT, NEC da NWC su na ganin shi ne ‘dan takarar da yake da kudin da za a iya amfani da su wajen cin zabe.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

A 2019, an ba Atiku Abubakar tuta a PDP, amma jam’iyyar ba ta iya samun nasara a kan APC ba.

2. Bukola Saraki

Jaridar ta ce Bukola Saraki yana cikin wadanda suka samu nasara da aka nemi fito da ‘dan takara tilo daga Arewa ta hanyar maslaha,ya fito ne daga Arewa ta tsakiya.

Akwai wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC da su ke tare da Saraki. Ana yi masa kallon gada tsakanin tsofaffin ‘yan siyasa da masu tasowa a zamanin nan.

Jam’iyyar PDP
Dr. Bukola Saraki a Kaduna Hoto: bukola.saraki
Asali: Facebook

3. Peter Obi

Peter Obi ya fito takara da kansa a wannan karo domin mulki ya koma kudu maso gabas. Ana kishin-kishin cewa sauran ‘yan takaran Ibo za su mara masa baya.

Obi yana cikin ‘yan siyasan kudu maso gabashin Najeriya da ya samu karbuwa sosai saboda jin labarin yadda ya gudanar da mulki da yake gwamna a Anambra.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m

4. Aminu Waziru Tambuwal

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyan yana cikin ‘yan gaba-gaba a zaben fitar da gwani a PDP. A zaben da aka yi a 2018, shi ne ya zo na farko bayan Atiku.

Da aka tashi fito da ‘dan takaran Arewa, Farfesa Ango Abdullahi bai dauki Aminu Waziru Tambuwal ba. A 2023 zai sauka daga kujerar Gwamnan Sokoto.

5. Nyesom Wike

Gwamnan jihar Ribas yana da kudin da zai iya tunkarar kowa wajen samun tikiti. Nyesom Wike yana ganin shi ya dace a ba tikiti tun da bai taba barin PDP ba.

Baya ga cewa bai taba sauya-sheka ba, Wike ya taka rawar gani wajen nada wasu shugabannin jama’iyyar, don haka yake ganin dole a saka masa abin da ya yi.

Ku na da labari cewa sauran masu neman takara PDP sun hada da; Mohammed Hayatu-Deen, Anyim Pius Anyim, Udom Emmanuel da kuma Ayodele Fayose.

Sai kuma irinsu; Nwachukwu Anakwenze, Dele Momodu, Sam Ohuabunwa, Cosmos Ndukwe, Charles Ugwu, Chikwendu Kalu, da Misis Oliver Tareila Diana.

Kara karanta wannan

Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

Da aka tantance 'yan takara, kwamitin David Mark ya cire Nwachukwu Anakwenze da Cosmas Ndukwe saboda wasu dalilai, aka su shiga zaben tsaida gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng