2023: Hukumar INEC ba za ta kyale Jam’iyyun siyasa 124 su tsaida ‘Yan takara ba

2023: Hukumar INEC ba za ta kyale Jam’iyyun siyasa 124 su tsaida ‘Yan takara ba

  • Da alama hukumar INEC mai zaman kanta, ba za ta ba wasu kungiyoyi damar shiga zabe mai zuwa ba
  • Akwai kungiyoyi sama da 100 da suke neman rajistar zama cikakkun jam’iyyu, har yau ba su dace ba
  • Idan ba ayi wa jam’iyya rajista shekara 1 kafin zabe ba, dokar zabe ba ta bata damar shiga takara ba

Abuja - Kungiyoyi fiye da 124 da suka nemi ayi masu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa, ba za su samu shiga zaben shekara mai zuwa na 2023 ba.

Punch a wani rahoto da ta fitar a ranar 8 ga watan Mayu 2022, ta bayyana cewa jam’iyyu 18 da INEC ta san da zamansu kurum za su iya yin takara.

A shekarar 2020 hukumar zaben ta soke rajistar wasu jam’iyyu saboda gazawarsu a zaben da ya wuce, hakan ta sa jam’iyyun siyasa 18 kadai aka bari.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

A 2021, babban jami’in hukumar INEC na kasa, Olayide Okuonghae ya tabbatar da cewa kungiyoyin siyasa akalla 101 sun nemi ayi masu rajista.

Olayide Okuonghae ya sanar da hakan ne bayan an aikawa hukumar da bukatar FOI kwanakin baya. INEC ba ta iya bayyana sunayen kungiyoyin ba.

Tsakanin Disamban na 2021 zuwa watan Maris na 2022, Punch ta ce an samu karin kungiyoyi 23 da suka tunkari INEC da nufin ayi masu rajistar siyasa.

Hukumar INEC
Shugaban hukumar INEC, Mahmud Yakubu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Masu neman rajista sun kai 124

A karshe dai an samu takardu daga kungiyoyi 124 su na neman a tabbatar da su a matsayin jam’iyyun siyasa ta yadda za su tsaida ‘yan takara a 2023.

Hukumar ta sanar da 97 daga cikin kungiyoyin akwai matsala tattare da sunaye ko tambarin da suka zaba ko, don haka ba za a iya masu rajista a haka ba.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

INEC ta fadawa kungiyoyi 11 da suke neman rajista cewa su canza suna, take ko tambari. An samu kungiyoyin da suka sake aikawa da takarda zuwa ga INEC.

Saura shekara 1 a shirya zabe

A halin yanzu saura kusan shekara daya a shirya babban zaben 2023. Yayin da ake wannan magana, wadannan kungiyoyi ba su samu cikakkiyar rajista ba.

Sashe na 75 na sabuwar dokar zabe ta ce dole ne duk wata jam’iyya ta samu rajistar da ake bukata akalla watanni 12 kafin zabe, abin da kungiyoyin suka gaza.

Gwamnan CBN ya ajiye aikinsa

Gwamnan jihar Ondo watau Rotimi Akeredolu yana ganin ba zai yiwu Gwamnan babban banki ya hada takarar siyasa da rike kujerar bankin CBN a lokaci daya ba.

A cewar Gwamnan Ondo wanda rikakken lauya ne, abin da Godwin Emefiele yake neman yi, ya saba dokoki da tsarin mulki, don haka ya kamata a tunbuke shi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng