Siyasar Kano: An samu wawakekiyar baraka tsakanin jagororin G7 da ke yakar Ganduje

Siyasar Kano: An samu wawakekiyar baraka tsakanin jagororin G7 da ke yakar Ganduje

  • Babu jituwa a yanzu tsakanin magoya bayan Barau Ibrahim Jibrin da na Malam Ibrahim Shekarau
  • Hakan ya jawo an samu rashin fahimta tsakanin ‘ya ‘yan G7 masu fada da Abdullahi Abbas a Kano
  • Ana zargin Shekarau ya lallaba ya saye fam a APC, yana ta kokarin yin sulhu da su Ganduje a asirce

Kano - Rahotanni na nuna ‘yan bangaren G7 a jihar Kano sun samu kansu a sabani. Punch ta kawo labarin nan a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu 2022.

An samu rikici ne a dalilin zargin da ake yi wa tsohon gwamna Ibrahim Shekarau na yunkurin sasantawa da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar ta ce ana tuhumar Malam Ibrahim Shekarau da sulhuntawa da Gwamnan Kano a asirce, da nufin ya zarce kan kujerar Sanata da yake kai a 2023.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

Idan ta tabbata, Sanata Shekarau ya hadu da Ganduje a boye, hakan zai zama cin amanar ragowar ‘Yan G7 da yake jagoranta wajen yaki da su Ganduje ne.

Sanata Barau ya fusata

Sanata Jibrin Barau wanda yana cikin manyan ‘yan wannan tafiya ta G7 ya fito fili yana sukar Malam Shekarau a kan abin da yake ganin juya baya ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jibrin Barau mai wakiltar Kano ta Arewa a majalisar dattawa yana ganin shugaban na su ya ci amanarsu a lokacin da suke da shari’a a gaban kotun koli.

'Yan siyasar Kano
Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau Hoto: @ahmed.princegandujiyya.9
Asali: Facebook

Magoya baya su na ta babatu

Rahoton ya ce magoya bayan wadannan manyan ‘yan siyasa biyu na jihar Kano su na cigaba da fito-na-fito da juna a dandalin sada zumunta na Facebook.

Masu wannan tunani su na ganin Shekarau ya yi son-kai, ya yi watsi da irinsu Hon. Shaaban Sharada da sauran ‘yan tawaren da ke fada da Abdullahi Abbas.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Magoya bayan Barau wanda yake harin kujerar Gwamna su na kiran Shekarau da ma-ci amana.

Ba haka ba ne - Shekarau

Amma Sule Ya’u Sule wanda yake magana da yawun bakin Sardaunan Kano ya nuna cewa Shekarau yana tare da G7 har gobe, bai juya masu baya ba.

Ya’u Sule ya shaidawa manema labarai cewa tsohon gwamnan ya sake yankar fam a jam’iyyar APC ne kamar yadda sauran ‘yan tawaren na G7 su kayi.

Kokarin dinke barakar APC

A farkon shekara, an ji yadda kwamitin riko na jam’iyyar APC a lokacin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya yi kokarin magance rikicin Kano.

Mala Buni ya kira taron gaggawa tsakanin bangarorin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau, har aka yi tunanin an cin ma matsaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng