Shugaban kasa a 2023: Osinbajo na kamun kafa da sarakuna

Shugaban kasa a 2023: Osinbajo na kamun kafa da sarakuna

  • Gabannin babban zaben 2023, yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban na ta kamun kafa a wajen masu ruwa da tsaki na kasar
  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya isa ga sarakuna a jihar Cross River inda ya nemi su mara masa baya tare da yi masa addu'a
  • Ya bayyana cewa zai iya kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta saboda gogewar da ya samu a tsawon shekaru bakwai da ya yi a matsayin mataimakin shugaban kasa

Cross River - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya nemi goyon bayan majalisar sarakunan gargajiya a jihar Cross River a kokarinsa na son zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Osinbajo wanda ya ziyarci majalisar sarakunan a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu a Calabar, ya ce sarakunan gargajiya wadanda sune suka fi kusa da mutane, suna taka muhimmiyar rawar gani a ci gaban kasar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Shugaban kasa a 2023: Osinbajo na kamun kafa da sarakuna
Shugaban kasa a 2023: Osinbajo na kamun kafa da sarakuna Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya fada masu cewa kasanvcewar ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru bakwai yana da tarin gogewa domin jagorantar kasar a matsayin shugaban kasa.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na zo nan ne domin neman goyon baya da addu’o’inku. Majalisar sarakuna ita ce mafi kusa da mutane. Tasiri da ikon da kuke da shi a yankuna daban-daban na da mahimmanci sosai.
“Na yi mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru bakwai, kuma a cikin lokacin nan, ya kasance tarin nasara kasancewar na san yadda ake mulki.
"Kwarewa na zai yi amfani a harkokin mulki, musamman wajen magance kalubalen kasarmu."

Da yake martani, Etinyim Etim-Okon Edet, shugaban majalisar sarakuna na Cross River, ya ce sarakunan za su taka rawa a kan wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Mista Edet ya ce za su tabbatar da ganin cewa an zabo wadanda suka cancanta a matsayin shugaban kasa, yan majalisar dokoki ta kasa, gwamnonin jihohi da kuma yan majalisar jiha a 2023, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

Ya ce:

"Muna son shugaban kasa, gwamnoni da 'yan majalisar dokokin kasa da za su mutunta 'yan Najeriya kuma su yi adalci ga dokokinmu.
“Bari mu tabbatar maka da goyon bayanmu yayin da kake zagayawa a cikin kasar. Kana cikin addu'o'inmu.
“Za mu yi amfani da hanyoyinmu na gargajiya don tabbatar da cewa an zabo wadanda suka cancanta a mukaman siyasa; muna yi maka fatan alheri.”

Ba za a tsawaita wa'adin zaben fidda gwani ba – INEC ga jam’iyyun siyasa

A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ce wa’adin da aka kayyade don gudanar da zaben fidda gwani na nan daram a kan Juma’a, 3 ga watan Yuni.

Hukumar zaben ta ce jam’iyyun siyasa na da sauran wata daya cif daga yau domin kammala zaben fidda gwaninsu, jaridar The Cable ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, INEC ta ce an baiwa dukkanin jam’iyyun siyasa guda 18 sanarwar da yakamata wanda ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng