Shugaban kasa: Fitaccen 'dan siyasar Arewa zai fito ya gwabza da su Osinbajo da Tinubu a APC

Shugaban kasa: Fitaccen 'dan siyasar Arewa zai fito ya gwabza da su Osinbajo da Tinubu a APC

  • Akwai yiwuwar Sanata Ahmad Ibrahim Lawan zai nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Kwanan nan za a ji Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya yanki fam na shiga zaben fitar da gwani a 2023
  • Zuwa yanzu Yahaya Bello ne kadai wanda ya fito daga bangaren Arewa da ke neman tikitin APC

Abuja – A makon nan shugaban majalisar dattawa na kasar nan, Ahmad Ibrahim Lawan zai bayyana nufinsa na neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Jaridar Premium Times ta ce idan abubuwa sun tafi yadda su ka kamata, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan zai sanar da Duniya wannan ne nan da wasu ‘yan kwanaki.

Ahmad Ibrahim Lawan ya dade yana harin wannan kujera, a karshe ya yi niyyar ya saye fam bayan bikin idi, yayin da Musulmai su ka gama azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

A ranar Juma’ar nan ne jam’iyyar APC za ta rufe saida fam din shiga takara. Ana sa ran shugaban majalisar kasar zai saye na takarar kujerar shugaban kasa kafin nan.

'Dan Arewa za a ba takara a 2023?

Idan har wannan labari ya tabbata, Lawan zai zama mutum na biyu daga Arewa da ke harin shugabancin Najeriya. Na farko shi ne Gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Ana tunanin wanda zai karbi mulki bayan Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023, zai fito ne daga kudu, don haka ne ‘Yan Arewa su ke ja baya a APC.

Dr. Ahmad Lawan
Ahmad Lawan a Majalisa Hoto: @NgrSenate / Tope Brown
Asali: Twitter

Amma sai aka ji sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya fito yana cewa ba su tsaida magana kan yankin da za a ba takara a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Jaridar Vanguard ta ce mutane ne sun hurowa Ahmad Lawan wuta ya nemi wannan kujera a matsayinsa na wanda ya fito daga Arewa maso gabashin Najeriya.

Daga cikin masu zugo ‘dan siyasar na jihar Yobe akwai mutanen yankinsa da kuma wasu Sanatoci. Tun 1999 ya ke majalisa, a 2007 ya zama Sanata a ANPP.

'Tun kwanaki aka nemi sayen fam'

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa a ranar Talatar da ta gabata ne Sanatan ya so ya saye fam, amma sai ya dakatar da maganar zuwa nan gaba saboda wasu dalilai.

Rahoton ya ce ana ta tattaunawa a kan wannan batu a ‘yan kwanakin nan a Abuja. Haka zalika a kasar Saudi Arabiya yayin da manyan ‘yan siyasa su ka hadu a Umrah.

Na kusa da Buhari za su yi takara

A wani rahoto da mu ka fitar a baya, an ji akwai wasu manyan masu rike da mukamai a gwamnatin tarayya da ke shirin yin takara a zabe mai zuwa da za ayi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Baya ga Farfesa Yemi Osinbajo, akwai Ministoci hudu da suke neman tikiti a APC. Haka zalika akwai Ministoci da Hadiman da za su nemi kujerar gwamnoni a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng