Jerin yan takaran shugaban kasa karkashin PDP 17 da ake tantancewa yau
Ana tsaka da ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin tarayya Abuja, ana tantance masu neman takarar kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.
Wannan tantancewa na gudana a Legacy House, sabanin Wadata House hedkwatar jam'iyyar ta kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.
Mutum 17 ne suka sayi Fom din takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.
Cikinsu akwai maza 16 da mace 1.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit Hausa ta tattaro muku jerin wadanda mutane 17:
1. Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa (1999-2007) kuma wanda ya wakilci jam'iyyar PDP a zaben 2019
2. Aminu Waziri Tambuwal
Tsohon Kakakin majalisar dokokin tarayya (2011-2015), gwamnan jihar Sokoto, shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma mataimakin shugaban kungiar gwamnonin Najeriya.
3. Bukola Saraki
Tsohon Gwamnan jihar Kwara (2003-2011) kuma tsohon shugaban majalisar dattawan tarayya (2015-2019)
4. Anyim Pius Anyim
Tsohon Shugaban majalisar dattawa (2000–2003), kuma tsohon Sakataren gwamnatin tarayya
5. Bala Abdulkadir Mohammed
Tsohon Sanata (2007-2010), tsohon Ministan birnin tarayya Abuja (201-2015) kuma gwamnan jihar Bauchi (2019 zuwa yanzu)
6. Nyesom Wike;
Tsohon Ministan Ilimi lokacin mulkin Jonathan, Gwamnan jihar Rivers (2019- yanzu)
7. Udom Emmanuel
Gwamnan jihar Akwa Ibom (2019-yanzu)
8. Peter Obi
Tsohon shugaban hukumar canjii SEC, tsohon gwamnan jihar Anambra (2007-2014) kuma dan takaran mataimakin shugaban kasa a 2019.
9. Ayodele Fayose
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti (2014–2018), (2003–2006)
10. Nwachukwu Anakwenze
Likita mazauni kasar Amurka
11. Dele Momodu
Shahrarren dan jarida, mai kamfanin mujallar Ovation
12. Mohammed Hayatu-Deen
Ma'aikacin banki kuma masanin tattalin arziki
13. Sam Ohuabunwa
Masanin ilmin hada magunguna
14. Chikwendu Kalu
Tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Abia
15. Cosmos Ndukwe
Tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Abia
16. Charles Ugwu
Magini rukunin gidaje
17. Tareila Diana
Mace daya tilo dake cikin yan takaran
Asali: Legit.ng