Da Dumi-Dumi: Tsohon shugaban majalisar Dattawa ya shiga tseren gaje Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Tsohon shugaban majalisar Dattawa ya shiga tseren gaje Buhari a 2023

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ken Nnamani, ya ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
  • Babban jigon ya bayyana wa duniya kwarewarsa na ya gaji Buhari, ya kuma roki APC ta rage makudan kuɗin da ta saka wa Fom
  • Ya ce Najeriya na bukatar shugaban da aka gwada aka san nagartarsa da gaskiyarsa kamar yadda aka san nashi

Abuja - Tsoohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, ya shiga tseren masu yunkurin gaje kujerar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a zaben 2023 ƙarƙashin APC.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Nnamani ya sanar da kudirinsa ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Jumu'a a birnin tarayya Abuja.

Babban jigon jam'iyya mai mulkin ya ce Najeriya na bukatar mutumin da aka gwada aka san gaskiyarsa kuma wanda zai iya haɗa kan yan ƙasa su fuskanci ƙalubale.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Shugaban APC ya yi tsokaci kan yankin da zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani.
Da Dumi-Dumi: Tsohon shugaban majalisar Dattawa ya shiga tseren gaje Buhari a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa tarihin muƙaman da ya rike na shugaban majalisar Dattawa da shugaban kwamitin sake fasalin kwansutushin da dokokin zaɓe sun nuna zai iya ɗora wa daga ayyukan da Buhari zai bari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"Muna bukatar shugabannin da aka gwada aka san gaskiyarsu, waɗan da zasu sabunta burikan dake zuciyar matasan Najeriya kuma su dawo mana da martabar da zamuyi gogayya da sauran ƙasashe."
"A 2023, kuna bukatar Ken Nnamani ya zo ya tallafa wajen haɗa kan Najeriya, inganta demokaraɗiyya, da kuma sake gina manyan ayyukan raya ƙasa da zasu haɓaka tattalin arziki da walwalar al'umma domin cigaban ƙasa."

Ya roki APC ta rage kuɗin Fom ɗin takara

Yayin da yake bayyana kwarewarsa da cancantarsa na ya gaji Buhari, Nnamani ya bukaci jam'iyyar APC ta rage makudan kuɗin Fom da ta zuga ga mai sha'awar neman takara.

Kara karanta wannan

Fusatattun Matasa sun fitittiki Sanata a mazabarta a Jos, sun kona motar yan jarida

A cewarsa kuɗin da APC ta sanya, kwata-kwata bai yi kama da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a zahirance a ƙasar nan ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa makudan kuɗin da jam'iyyun siyasa ke zuga wa yan takara wajen siyan Fam na bukatar a sake tunani na musamman a kansa.

Ya jaddada cewa da bukatar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta shigo ciki, "ta ƙayyade kudin Fom da kuɗin da yan takara ke ƙashewa wajen kanfe."

Tsohon Sanatan zai fafata da fitattun yan takara da suka haɗa da Bola Tinubu, gwamna Yahaya Bello, gwamna Dave Umahi, da sauran su a zaɓen fidda gwani na APC.

A wani labarin kuma Tsohon kakakin majalisa ya bayyana shirin da yake na gaje Buhari, zai lale miliyan N100m

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Dimeji Bankole, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya sake tsoma baki kan yaƙin Rasha-Ukarine a wurin buɗe bakin Ramadan

Wani makusancin Bankole ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya fara shirye-shirye, kuma zai karɓi Fom mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262