'Ba Tinubu bane' Osinbajo ya faɗi gaskiyar wanda ya gaya masa an zaɓe shi mataimakin Buhari

'Ba Tinubu bane' Osinbajo ya faɗi gaskiyar wanda ya gaya masa an zaɓe shi mataimakin Buhari

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya fara sanar da shi an zaɓe shi mataimaki
  • Mataimakin shugaban ƙasan ya ce yana cikin aiki kan wata shari'a a Abuja a Disamba 2014, labari ya zo masa cikin mamaki
  • A yanzu dai, Osinbajo na ɗaya daga cikin mutanen dake hangen kujerar shugaban ƙasa karkashin APC

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce labarin an zaɓe shi ya zama abokin takarar Muhammadu Buhari, ya zo masa da mamaki matuƙa.

Osinbajo ya ce yana cikin aiki kan shari'ar wani ɗan majalisa da ya sauya sheka a Kotun Ƙoli ne sai labarin zaɓarsa ya zo masa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Shugaba Buhari tare da Osinbajo.
'Ba Tinubu bane' Osinbajo ya faɗi gaskiyar wanda ya gaya masa an zaɓe shi mataimakin Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Osinbajo ya ba da labarin yadda dare ɗaya Allah kan yi bature yayin da ya karbi bakuncin wasu mutane wurin cin abincin buɗe baki a gidansa dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Kara karanta wannan

Ba don jajircewar Buhari ba da rashin tsaron Najeriya ya fi haka muni, Gwamnan dake son takara

Mataimakin shugaban ƙasa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina cikin aiki kan shari'a a Abuja ranar 18 ga watan Disamba, 2014 yayin da na karɓa kiran wayar Rauf Aregbesola da karfe 1:00 na dare cewa za su zo Legas su ɗauke ni."
"Na ce masa ina Abuja, ya ce ya yi kyau saboda an zaɓe ni mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, na tambaye shi ta ya kuke zaɓen mutane."

Mataimakin shugaban ya ce bayan kammala aikinsa na ranar sai ya koma masaukinsa, ya cire kayan jikinsa, ya fara tunanin, "Da yuwuwar karo na karshe kenan da zan sa kayan nan."

Me ya faru bayan faruwar haka?

Osinbajo ya cigaba da cewa Mista Aregbesola, ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan Ogun, ya zo har gida ya ɗauke shi zuwa wurin ɗan takara, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Mutumin da Shugaba Buhari ke son ya gaje shi zai ba kowa mamaki, Sanatan dake son takara

Ya ce ya na ba da wannna labarin ne domin yan Najeriya su ƙara gane cewa rayuwar mutum kan iya canzawa lokaci guda.

A wani labarin kuma An tsaurara matakan tsaro yayin da yan takara suka fara dira Sakatariyar PDP

Jami'an tsaro sun mamaye Sakatariyar PDP dake Patakwal a jihar Ribas yayin da ake gab da fara tantance yan takara.

Yan sanda, DSS da sauran jami'an tsaro sun hana kowa shiga har sai ka gabatar da katin shaida ko da ɗan jarida ne kafin ka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262