'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo

'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo

  • Farfesa Yemi Osinbajo yace 'dana mulkin da yayi lokacin da maigidansa ke jinya a Landan alama ne dake nuna shi Allah ke son ya gaji Buhari
  • Mataimakin shugaban kasa ya tafi jihar Oyo yakin neman zabe wajen deleget din jihar gabanin zaben fidda gwani
  • Har yanzu ana cece-kuce kan niyyar takarar Yemi Osinbajo saboda tsohon maigidansa Tinubu yana nema

Ibadan - Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa aikin da yayi tare da Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi kwarewa sosai wajen gudanar da mulkin al'umma.

Osinbajo ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Ibadan, birnin jihar Oyo yayinda ya ziyarci deleget din jam'iyyar dake jihar, rahoon TheCable.

Yace Buhari ya bashi daman aiwatar da wasu ayyuka masu muhimmaci a kasashen waje, saboda haka zai yi amfani da kwarewar da ya samu wajen mulkan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa na fitar da N100m don sayawa Tinubu fom din takara, Attajirin Dan kasuwa

Yace:

"A ranar 11 ga Afrilu, na ayyana niyyar takara kujerar shugaban kasar Najeriya. Na yi aiki matakin gwamnatin tarayya shekaru bakwai da suka shude yanzu."
"Kamar yadda kuka sani, na yi mukaddashin shugaban kasa na 'dan lokaci yayinda shugaban kasa ke jinya. Dukkan abubuwan da na koya matsayin mataimakin shugaban kasa na nuna min cewa na cancanci tafiyar da lamuran kasar nan matsayin shugaban kasa."
"Ubangiji ba ya kuskure; da gayya yake abubuwansa. Dukkan damammakin da ya bani na fahimtar shugabanci, ba a banza bane, wajibi ne nayi amfani da su."

Yemi Osinbajo
'Dana mulkin da nayi lokacin da Buhari ke jinya yasa nike ganin na cancanci zama shugaban kasa: Osinbajo Hoto: BBC Pidgin
Asali: Facebook

Na miƙa wuya Mataimakin shugaban kasa ne zai gaji Buhari a 2023, Sanatan APC daga Kano

Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya karɓi ragamar kungiyar cigaba (TPP), gamayyar kungiyoyin magoya baya masu yaɗa manufar mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Ku kwantar da hankulanku, yafewa Dariye da Nyame ba matsala bane - Buhari

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Sanata Gaya, ya ce burin Osinbajo ba na ƙashin kansa bane, amsa kiran al'umma ne na tsayawa takara.

Sanatan ya ƙara da cewa ya na da kwarin guiwa Osinbajo ne zai gaji kujerar shugaba Buhari a zaɓen 2023, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng