Dalilin da ya sa na fitar da N100m don sayawa Tinubu fom din takara, Attajirin Dan kasuwa
- Mutumin da ya zuge milyan dari don sayawa Tinubu fom din takara kujerar shugaban kasa ya bayyana dalilin yin haka
- Aminu Suleiman, wanda attajiri ne kuma dan gidan sarauta a Kebbi yace alkawari ne ya cika
- Wannan na zuwa ne yan sa'o'i bayan jam'iyyar All Progressives Congress APC ta sanar da farashin Fom
Attajirin dan kasuwa dan jihar Kebbi, Aminu Sulaiman, ya bayyana dalilin da yasa ya zuge milyan dari don sayawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu tikitin takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC.
Aminu Sulaiman, wanda shine Dirakta Janar kungiyar goyon bayan Tinubu watau Tinubu Support Organisation (TSO) ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar da yammacin Laraba.
Ya ce ai dama tuni ya yi alkawarin tabbatar da cewa Tinubu ya yi takara kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba sai Tinubu ya hau mulki.
Yace:
"Ku tuna cewa ni Hanarabul Aminu Suleiman, Yarima kuma dan kasuwa daga jihar Kebbi, na yi alkawarin kai Asiwaju kotu idan yaki takara kuma tunda ya amsa kiranmu, na ga ya zama wajibi in jaddada cewa na fitar da N100m don tabbatar da cewa ya zama shugaban kasar nan a 2023."
"Yanzu mun fara kuma Insha Allahu Bola Tinubu zai zama shugaban kasa a 2023."
APC ta sanar da farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar
APC ta ce naira milyan dari kowani dan takaran shugaban kasa zai biya don yankan Fom.
Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.
N10m za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.
Za'a fara sayar da Fam din daga ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Bayan sanar da farashin, jam'iyyar APC ta ce duk matashi mai kasa da shekaru 40 a duniya an yi masa rahusa ya biya rabin kudin fam.
Asali: Legit.ng