Farashin fam, ranar zaben fidda gwani da sauran abubuwa 3 da majalisar zartaswar APC ta yanke shawara kansu
Majalisar zartaswa NEC ta Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi zamanta na 11 ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu, 2022 a dakin taron Transcorp dake birnin tarayya Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari; mataimakinsa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa da na wakilai, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, duk suna hallare.
Hakazalika gwamnonin jam'iyyar APC da sabbin shugabannin jam'iyyar da aka zaba a taron gangamin da akayi a watan Maris.
Majalisar NEC ke da hakkin yanke shawarar karshe kan abubuwa masu muhimmanci na jam'iyyar.
A zaman ranar Laraba, Legit ta tattaro muku a takaice, jerin abubuwa biyar da aka yi a taron:
1. Ta dankawa kwamitin gudanarwa ikon amfani da karfinta na tsawon kwanaki 90
Kada kowa yazo da waya: Aisha Buhari ta shirya liyafa ga 'yan takarar shugaban kasa a dukkan jam'iyyu
Abin farko da majalisar zartaswar tayi shine mikawa kwamitin gudanarwa ta jam'iyyar karfin tafiyar da harkokin jam'iyyar na tsawon kwanaki 90.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mambobin kwamitin gudanarwa sun hada da Shugaban uwar jam'iyya Abdullahi Adamu, mataimakansa, da sauran wadanda aka zaba.
2. Ta sanar da ranar gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
Majalisar ta amince da ranar 30 da 31 ga Mayu matsayin ranakun gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023.
Wannan na cikin sanarwar Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barista Felix Morka, bayan taron majalisar NEC da ya gudana a Abuja ranar Laraba.
Barista Morka yace kuma ranar 18 Mayu za'a gudanar da zaben fidda gwanin gwamnoni.
3. Ta yi watsi da tsarin yar tinke, zaben deleget za'a yi
Ta yi watsi da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023 sabanin yadda tayi a zaben 2019.
Jam'iyyar ta yanke shawarar amfani da deleget wajen zaben wanda zai wakilci jam'iyyar a zaben shugaban kasa.
Jam'iyyar APC na da Deleget 7,800.
Yayinda jihar Kano tafi yawan deleget, Abuja ke da mafi karanci.
4. Ta sanar da farashin da zata sayar da fam ga duk wadanda ke son takarar
APC ta ce naira milyan dari kowani dan takaran shugaban kasa zai biya don yankan Fom.
Na gwamna kuwa, za'a sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata zasu kashe N20m.
N10m za ta sayar da Fam ga masu neman kujerar yan majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.
Za'a fara sayar da Fam din daga ranar 22 ga Afrilu, 2022.
5. Ta yiwa matasa yan kasa da shekaru 40 rahusan kudin fam, ta ce su biya rabin kudin
Bayan sanar da farashin, jam'iyyar APC ta ce duk matashi mai kasa da shekaru 40 a duniya an yi masa rahusa ya biya rabin kudin fam.
Asali: Legit.ng