Na hannun daman gwamna Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamna a 2023

Na hannun daman gwamna Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamna a 2023

  • Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya janye daga tseren takarar gwamnan jihar a zaɓe mai zuwa
  • Bayanai sun nuna cewa Alhaji ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gana wa da mai girma gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
  • Hakan na zuwa ne dai-dai lokacin da masu hangen kujerar a cikin gwamnati ke cigaba da yin murabus don biyayya ga doka

Kano - Sakataren gwamnatin jihar Kano, (SSG), Alhaji Usman Alhaji, ya janye daga cikin jerin masu tseren takarar gwamna a jihar a zaɓen 2023.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar fifita shugabanci mai kyau, Alhaji Dan’azumi Gwarzo, ya fitar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin Kano ya janye daga takara.
Na hannun daman gwamna Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamna a 2023 Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya ce matakin janyewa daga takarar ya biyo bayan wani taro da SSG ya yi da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda aka ja hankalinsa ya janye saboda dabarun siyasa.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Biyo bayan ganawa tsakanin gwamna Abdulahi Ganduje, Sakataren gwamnati da shugabannin ƙungiyar mu, mun cimma matsayar SSG ya yanje daga takarar gwamna."

Daga nan, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su maida hankali kan harkokin da zasu kawo cigaba a jihar Kano.

Wannan na zuwa ne bayan gwamna Ganduje ya ƙi amince wa da murabus ɗin Sakataren da kuma wasu kwamishinoni.

Mambobin majalisar gwamnatin Kano da suka haɗa da kwamishinoni da hadimai sun fara bin umarnin gwamna na aje mukaman su don maida hankali ga niyyarsu ta takara.

Ɗan takara shugaban ƙasa a APC ya gigice da jin kudin Fam

A wani labarin na daban kuma Mai neman APC ta ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya kaɗu da jin kuɗin Fam ɗin takara Naira Miliyan N100m.

Kara karanta wannan

2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna

Da yake martani kan kuɗin Fam, Matashin ɗan takarar ya nuna kaɗuwarsa da yawan su makudan kuɗin.

Da yake tsokaci kan lamarin a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter, Garba, wanda ya nemi takara a 2019, ya rubuta cewa, "Miliyan N100m kuɗin Fam! Lallai ."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262