Garba Shehu: Abin da ya sa aka ga Buhari ya yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke kurkuku

Garba Shehu: Abin da ya sa aka ga Buhari ya yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke kurkuku

  • An tattauna da Malam Garba Shehu a game da afuwar da shugaban kasa ya yi wa wasu mutum 160
  • Malam Garba Shehu yana cikin Hadiman da ke magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari
  • A cewar kakakin shugaban kasar, sai da majalisar koli tayi tunani kafin a yafewa wadannan mutane

Abuja - Jaridar Daily Trust tayi hira da mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, inda aka tattauna da shi kan sha’anin kasa.

A hirar da aka yi da Mai ba Muhammadu Buhari shawara, an bukaci jin dalilin gwamnatinsu na yin afuwa ga wadanda aka samu da laifin cin dukiyar kasa.

Da yake jawabi, Malam Garba Shehu ya ce majalisar koli tayi tunani kafin ta dauki wannan mataki. A cewarsa, ba haka nan Buhari ya yi abin da kai ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Kwata-kwata babu adalci a Najeriya, dole a sha wahala

Hadimin ya ce a kan haka aka ki yin afuwa ga wani wanda kotu ta yankewa daurin shekara 120. Majalisar ta ga cewa bai dace a saki irin wannan mutum ba.

Me Garba Shehu ya fada?

“Akwai abubuwa biyu a a nan, na farko, ba na so in yi magana a game da tulin karfin da dokar kasa a karkashin sashe na 175 ya ba shugaban kasa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Shugaban kasa yana da ikon da zai iya yin afuwa a kan kowane irin laifi ba tare da wani sharadi ba. Amma a nan, ba haka aka yi ba, an bi matakai.”
Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari wajen buda baki Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

“Daga cikin ka’idojin shi ne rashin lafiya ko tsufa. Majalisar koli da ta goyi bayan shugaban kasa, ta na dauke da shugabannin kasar nan masu tunani.”

- Garba Shehu

An sa siyasa a lamarin

An rahoto Mai magana da yawun shugaban kasar yana cewa mutane za su siyasantar afuwar da aka yi, ya ce wannan ce al’adar al’umma har a Amurka.

Kara karanta wannan

Babu Nadamar Komai Saboda Tunbuke Ni, Kuma Ba Zan Yi Shiru Ba Inji Sanusi II

“Idan shugaban Amurka ya yi wa wasu afuwa, sai a ce siyasa ce. Ita kan ta kunyar daure mutum ta isa shari’a, a wasu kasashen wannan kawai hisabi ne”

- Garba Shehu

Akwai adalci a afuwar?

Jaridar ta nemi jin dalin fito da tsofaffin gwamnonin da ke tsare, a yayin da kananan barayin da suka saci akuya suke cigaba da zama a gidajen gyaran hali.

Shehu ya ce mutane sun karkata ne a kan afuwar da shugaban Najeriya ya yi wa Jolly Nyame da Joshua Dariye, amma an yi wasu mutanen da-dama afuwa.

“A cikin mutane 160, za ku yi mamakin jin cewa akwai sauran kananan mutane da ‘yan jarida ba su dama da su ba, shiyasa babu wani mai maganar su.”

Hadimin Buhari zai tafi majalisa

An samu rahoto Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmaad ya na shirin takarar ‘dan majalisa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Yadda dalibin jami'a ya kama sana'ar siyar da shayi don yakar zaman kashe wando

Malam Bashir Ahmaad ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a ranar Talata. Ahmaad zai nemi kujerar Gaya/Ajingi/Albasu (Kano) a majalisar wakilan tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng