Da duminsa: APC ta sanar da ranar gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa
- Jam'iyyar APC a ranar Laraba ta yanke shawara kan ranar da zata gudanar da zaben fidda gwanin yan takararta
- Akalla mutum goma sha biyar suka alanta niyyar gajen shugaba Buhari karkarshin jam'iyyar APC
- Za'a gudanar na kujeran shugaban kasa mako guda bayan gudanar da na gwamnoni
Abuja - Majalisar zartaswa NEC ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta amince da ranar 30 da 31 ga Mayu matsayin ranakun gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023.
Wannan na cikin sanarwar Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barista Felix Morka, bayan taron majalisar NEC da ya gudana a Abuja ranar Laraba.
Barista Morka yace kuma ranar 18 Mayu za'a gudanar da zaben fidda gwanin gwamnoni, rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin sunayen wadanda suka ayyana niyyar takara karkashin jam'iyyar APC:
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Prof Yemi Osinbajo
Chief Rotimi Amaechi
Dr. Chris Ngige
Governor Yahaya Bello
Ibinabo Joy Dokubo
Ihechukwu Dallas-Chima
Senator Orji Uzor Kalu
Engr Dave Umahi
Rev Moses Ayom
Senator Rochas Okorocha
Gbenga Olawepo-Hashim
Ibrahim Bello Dauda
Dr. Tunde Bakare
Tein Jack-Rich
Jam'iyyar APC ta yi watsi da tsarin yar tinke, zaben deleget za'a yi, Kano ta fi yawan deleget
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023 sabanin yadda tayi a zaben 2019.
Jam'iyyar ta yanke shawarar amfani da deleget wajen zaben wanda zai wakilci jam'iyyar a zaben shugaban kasa.
An yanke shawarar haka ne a taron Majalisar zartaswa NEC ta 11 da ke gudana a Transcorp Hotel dak birnin tarayya Abuja.
Kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya bada zabi uku na yadda za'a gudanar da zaben fidda gwani.
Asali: Legit.ng