Da Dumi-Dumi: Bayan Sanata Adamu, wani babban Jigon APC ya yi murabus daga kujerarsa
- Donald Ojogo, ya miƙa takardar murabus ɗinsa daga gwamnatin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ba tare da jinkiri ba
- Gwamna Akeredolu, idan ba ku manta ba ya ba hadimansa dake niyyar takarar siyasa awanni 48 su aje muƙamansu
- Ya yi murabus ne domin ya nemi kujerar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ilaje/Ese-Odo a majalisar wakilan tarayya
Ondo - Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai, Mista Donald Ojogo, ya yi murabus daga gwamnatin gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.
Idan baku manta ba, gwamnan jihar Ondo, a ranar Talata 12 ga watan Afrilu 2022, ya umarci masu rike da muƙaman naɗi da Ofisoshin gwamnati waɗan da ke da niyyar neman takara a kowane mataki su yi murabus ranar ko kafin Alhamis.
Gwamna Akeredolu ya ba da wannan umarnin ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Afrilu, kuma da sa hannun Sakatariyar gwamnati, Princess Oladunni Odu.
A wata sanarwa da Ofishin yaɗa labarai na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen kwamishinan ya aike wa Legit.ng Hausa, ya ɗauki wannan matakin ne domin neman kujerar mamba a majalisar wakilai ta tarayya.
Sanarwan ta ce:
"Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ondo, Honorabul Donald Ojogo, ya yi murabus yayin da goyon bayan da yake samu na ya nemi mamba a majalisar wakilan tarayya ke ƙara ƙaruwa."
"Zai bar Ofis daga ranar 14 ga watan Afrilu, 2022. Ya yaba wa gwamna Oluwarotimi Akeredolu, SAN, bisa amince masa, ya kuma tabbatar da cewa tafiyarsu a siyasa yanzu aka fara."
Kundin dokokin zaɓe 2022 ya tanadi cewa duk wani mai rike da muƙamin gwamnati ko naɗin siyasa dake hangen wata kujerar siyasa ko Deleget ya yi murabus daga kan muƙaminsa.
Gwamna da Sanata zasu tsiga tseren takara
A wani labarin kuma Gwamnan Fayemi na APC da Sanata Amosun zasu ayyana takarar shugaban ƙasa, sun sanar da Buhari
Jiga-Jigan siyasa musamman masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun shirya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023.
Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanata Ibikunle Amosun na shirin sanar da shirinsu na neman kujera lamba ɗaya.
Asali: Legit.ng