‘Yan Majalisar dokoki 2 sun bada sanarwar sauya-sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP
- ‘Yan Majalisar dokoki biyu su ka bada sanarwar sauya-sheka daga jam’iyyar APC a jihar Anambra
- Honarabul Douglas Egbuna mai wakiltar mutanen yankin Onitsha ta Arewa ya fice daga jam'iyyar
- Haka zalika Honarabul John Nwokoye ya bayyana cewa ya zama cikakken ‘dan jam’iyyar PDP daga yau
Anambra – A yau ne wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Anambra, su ka bada sanarwar ficewarsu daga jam’iyyar APC, inda suka koma PDP.
Jaridar The Guardian ta kawo labarin sauya-shekar a ranar Talata, 11 ga watan Afrilu 2022.
Wadanda suka zabi su fice daga APC su ne Douglas Egbuna da John Nwokoye. Sun kasance masu wakiltar mutanen mazabun Onitsha da Akwa ta Arewa.
Honarabul Douglas Egbuna ya shaidawa abokan aikinsa cewa daga yanzu ya tashi daga ‘dan jam’iyyar APC, amma bai fadi dalilin canza shekar ba.
Kafin yadda The Eagle ta kawo rahoto, kafin yanzu, Hon. Egbuna shi ne mataimakin shugaban mai tsawatarwa a majalisar dokokin na jihar Anambra.
A kan mene su ka canza sheka?
“Ina mai farin ciki sanar da sauya-sheka ta daga APC zuwa PDP saboda dalilan da ni kadai ne na sansu.” - Douglas Egbuna
Haka zalika shi ma Hon. Nwokoye ya bi Egbuna zuwa jam’iyyar PDP, ya tabbatar da cewa bai da wata alaka da jam’iyyar APGA mai mulki da kuma APC.
“Ina so in sanar da sauya-sheka ta zuwa PDP saboda wasu dalilai na kai na. Daga yanzu nib a ‘dan APGA ba ne, kuma ni ba ‘dan jam’iyyar APC ba ne.”
- John Nwokoye
PDP ta yi lale maraba da su
Shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar, Hon. Onyebuchi Offor ya karbi sababbin shiga jam’iyyar PDP da hannu biyu, ya na mai yi masu maraba.
Hukumar dillacin labarai ta ce da wannan sauya-sheka da aka yi, 'yan PDP a majalisar dokokin sun kai takwas a lokacin da ake shirin zaben fitar da gwani.
Bayan nan shugaban majalisar dokokin Anambra, Rt. Hon. Uche Okafor ya daga zama. Sai ranar 26 ga watan Afrilun nan ‘yan majalsia za su sake haduwa.
Takarar Osinbajo ta barka APC
Mu na da labari cewa Hadimin Gwamnan Legas, Joe Igbokwe ya yi kashedi ga ‘Yan siyasar da Bola Tinubu ya kawo siyasa, su ke neman yin takara da shi.
Joe Igbokwe ya bukaci irinsu Yemi Osinbajo su hakura da batun takara, haka zalika duk gwamnoni su sallamawa Tinubu a zaben tsaida 'dan takara.
Asali: Legit.ng