Jigon PDP ya bayyana abin da zai tarwatsa Jam’iyyar adawar a zaben Shugaban kasa

Jigon PDP ya bayyana abin da zai tarwatsa Jam’iyyar adawar a zaben Shugaban kasa

  • Bode George ya gargadi jam’iyyar PDP da cewa su yi hattara da rikicin cikin gida a Legas da Kano
  • Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ya ce rikici a jihohin na iya hana PDP cin zabe a 2023
  • George ya rubutawa Dr. Iyorchia Ayu takarda cewa a soke zaben shugabannin da aka yi a Legas

Lagos - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar hamayya ta PDP, Olabode George ya ja-kunnen Dr. Iyorchia Ayu da cewa ya saurari koke-koken ‘yan jam’iyya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Cif Olabode George ya na cewa akwai bukatar shugaban PDP ya dinke barakar da ta ke Legas da Kano masu dinbin jama'a.

A wata hira da aka yi da babban ‘dan siyasar, ya fadi cewa rikicin cikin gidan da ake da su, za su iya kawowa jam’iyyar adawar cikas a zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Dokubo Asari ya caccaki Gwamnan PDP, ya ce takararsa a 2023 ba za ta kai labari ba

George ya na ganin muddin ba a magance matsalolin ba, PDP za ta tashi aiki a 2023. A cewarsa, bai dace a kyale rikici a Kano da Legas masu tulin kuri’u ba.

Zaben shugabanni PDP na Legas

Har ila yau, an rahoto George ya na sukar zaben shugabannin jam’iyyar PDP na reshen jihar Legas da gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya shirya a kwanakin baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan ana so a zauna lafiya a Legas, jigon na PDP ya ce dole ayi watsi da wannan zaben da aka yi.

Jigon PDP
Bode George ya na so mulki ya bar Arewa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Phillip Aivoji shi ne ya doke Amos Fawole a zaben da aka gudanar. Ana tunanin Fawole shi ne yake tare da jiga-jigan jam’iyyar PDP, har da irinsu Bode George.

A cewarsa, kananan hukumomi uku kurum hukumar INEC ta ba damar su yi zabe a Legas, amma a karshe sai PDP ta gudanar da duka zaben shugabannin a haka.

Kara karanta wannan

An jefa jam’iyyar PDP cikin ala-ka-kai a Kano, kotu tace a ruguza duka sababbin shugabanni

Gwamna Diri ya sanar da cewa wasu dabam ne suka lashe zabe. Hakan ta sa George ya rubuta takarda ga Dr. Ayu, ya na ce masa ba za a iya cin zabe a haka ba.

A maida mulki Kudu

Jaridar Vanguard ta rahoto George ya na sake nanata batun mika mulki zuwa yankin kudu a 2023. A cewarsa wannan shi ne ya zo daidai da tsarin mulkin Najeriya.

George ya ce duk da yanzu ba PDP ta ke mulki ba, ya kamata ta tsaida ‘dan kudu ne a 2023, ganin cewa mutanen Arewa sun fi dadewa a mulki tun daga 1960 zuwa yau.

Osinbajo zai yi takara

A yau ne za a ji labari Yemi Osinbajo zai shiga sahun masu neman tikitin APC. Wannan karo zai goge raini tare da tsohon mai gidansa a siyasa watau Bola Tinubu.

Rahotanni sun ce Mataimakin shugaban kasa zai kawo wani irin sabon salon yakin neman zaben shugaban kasaa Najeriya kamar yadda ‘Yan kasa za su gani an jima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng