Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari

Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari

  • Shugaban matasan APC reshen yan Najeriya mazauna Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa, ya koma NNPP
  • Dakta Usman Shehu, ya ce tsohuwar jam'iyyarsa ta gaza cika wa yan Najeriya alƙawurran da ta ɗauka a yaƙin neman zaɓe
  • Yace ƙasa ta lalace ba tsaro, matasa ba aikin yi, tattalin arziki ya raunata da sauran matsaloli duk a gwamnatin APC

Kano - Shugaban matasan jam'iyyar APC reshen ƙasar Burtaniya, Dakta Usman Tijjani Shehu, ya fice daga jam'iyya mai mulki, ya koma NNPP mai kayan marmari.

Ya tabbatar da murabus ɗinsa a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban APC na gundumarsa a ƙaramar hukumar Kabo, jihar Kano kuma ya tura wa APC reshen Burtaniya kwafinta.

Jam'iyyar APC ta yi rashi a Kano.
Shugaban matasan jam'iyyar APC a Uk ya yi murabus, ya koma NNPP mai kayan marmari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Haka nan kuma Daily Trust ta samu kwafin takardar da tsohon shugaban matasan ya rubuta domin tabbatar da murabus ɗinsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP sun fice daga jam'iyya, sun koma NNPP ta Kwankwaso

Meyasa ya fice daga APC?

Tsohon shugaban matasan APC na neman takarar ɗan majlisar wakilai mai wakiltar yankunan Kabo/Gwarzo a majalisar tarayya.

Ya ce ya ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda ya gano gaskiya cewa ta gaza wa yan Najeriya kuma ba zata iya cika alƙawurran da ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe ba.

Ya kuma zargi jam'iyya mai mulki da ɓarnata baki ɗaya cigaban Najeriya ta ko wane fanni, kuma ta watsar da matasa ba ta samar musu damarmaki.

Dakta Shehu ya ce:

"Halin da ake ciki a ƙasa yanzu haka ba bu aikin yi, kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta na cikin yajin aiki, kalubalen tsaro sun yi yawa, wuraren duba lafiya sun yi ƙaranci, tattalin arziƙi ya lalace, ba matasa a shugabanci."

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

A wani labarin kuma Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki

Tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Gombe, Barista Abdulƙadir Yahaya, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

Tsohon mashawarci kan harkokin siyasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda ɗumbin ayyukan cigaba da gwamna ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262