Abin da Gwamna El-Rufai ya fadawa Tinubu ido-da-ido a game da takarar da zai yi a 2023
- Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin Bola Tinubu bayan harin jirgin Kaduna-Abuja
- Malam Nasir El-Rufai ya godewa gudumuwa da damuwar da jigon na APC ya nunawa al’ummarsa
- Amma duk da haka, da yake maganar 2023, sai Gwamnan ya yi addu’ar Ubangiji ya ba nagari mulki
Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya hadu da Asiwaju Bola Tinubu yayin da ‘dan siyasar ya zo yi masa ta’aziyyar harin da aka kai kwanaki.
‘Yan ta’adda sun tare jirgin kasan Kaduna-Abuja har sun yi ta’adi a makon da ya wuce. Daily Trust ta ce hakan ta sa Bola Tinubu ya zo yin Allah-kyauta dazu.
Mai girma gwamnan jihar Kaduna ya karbi Asiwaju Bola Tinubu, amma kuma ya ki nuna goyon bayansa kai-tsaye a game da takarar da ‘dan siyasar zai yi.
Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m
Bola Tinubu ya na cikin wadanda suka fara bayyana shirin neman kujerar shugaban kasa a 2023.
Malam El-Rufai ya ji dadin yadda Tinubu ya nuna damuwarsa ga mutanen da aka kai wa hari, ya ce gwamnatin jihar Kaduna ba za ta taba mantawa da shi ba.
Amma rahoton ya ce duk wannan bai sa Gwamnan ya nuna goyon bayansa ga jagoran na APC ba, sai dai ya yi addu’a ga Ubangiji da ya yi wa 'Yan Najeriya zabi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An shiga wani irin hali a yau
“Mun san da burinka na son zama shugaban kasar nan, mu na sa ran mu cigaba da tattaunawa domin taimakawa wannan burin.”
“Najeriya ta na halin gargara, ta shiga wani yanayi, kuma dole ne mu dauki matakai masu zafi domin zaben shugabanni na kwarai."
- Mallam Nasir El-Rufai
El-Rufai ya ce ya zama dole a zakulo shugabannin da za su iya ceto kasa daga halin da ake ciki.
“Wadannan matsaloli ne da ‘Dan Adam zai iya shawo kan su. Ina addu’a ga Ubangiji ya yi wa Najeriya zabi da wanda ya fi dacewa...”
“Domin a samu kasa mai zaman lafiya, cigaba da hadin-kai, sannan wanda za a iya yin misali da ita, wanda za ta yi kowa adalci.”
- Mallam Nasir El-Rufai
Da yake jawabinsa, Tinubu bai yi magana a kan siyasa ba, sai dai a kan abin da ya shafi tsaro. Legit.ng Hausa ta fahimci ziyarar ta jawo mutane su na ta surutu.
Wike da kusoshin PDP sun je Minna
A jiya aka ji cewa Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya yi mulkin soja a Najeriya, ya yi zama na musamman da tawagarsu Gwamna Nyesom Wike a garin Minna.
Abdussalami Abubakar ne ya yi wa Gwamnonin na PDP, da Sanata Kashim Imam, da su Suleiman Nazifi iso a wajen Ibrahim Babangida domin su tattauna.
Asali: Legit.ng