Fice Wa Daga APC Ba Shine Mafita Ba, Lai Mohammed Ya Roki Fusatattun 'Yan Jam'iyyar a Kwara
- Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya roki fusattun ‘yan jam’iyyar APC da ke Jihar Kwara akan su sauya tunani akan batun barin jam’iyyar
- Ministan ya fadi hakan ne ta wata takarda wacce ya saki ranar Talata inda ya roki wadanda suka sauya sheka da su dawo jam’iyyar
- A cewarsa mutane sun janyo hankalinsa akan yadda wasu suke ta sauya sheka suna komawa jam’iyyar SDP daga jam’iyyar APC
Kwara - Lai Mohammed, ministan al’adu da labarai ya roki fusatattun ‘yan jam’iyyar APC da ke Jihar Kwara akan sauya tunani dangane da shirin barin jam’iyyar APC a jihar, The Punch ta ruwaito.
Ministan wanda dan asalin Jihar Kwara ne, ya yi wannan kiran ta wata takarda wacce ya saki a ranar Talata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bukaci wadanda suka sauya shekar akan su sauya tunani dangane da barin jam’iyyar su kuma daura dammarar shirin zaben 2023 da ke karatowa.
Ya ce su kara hakuri su kuma hada kai
Kamar yadda The Punch ta bayyana, Mohammed ya kada baki ya ce:
“An janyo hankali na akan rahotannin jama’a na batun sauya shekar wasu mabiyana na jam’iyyar APC na Jihar Kwara da suke komawa SDP.
“Ina son in yi bayani akan cewa duk da yadda mabiyanmu suke cikin kunci da takaicin yadda gwamnan Jihar Kwara yake tafiyar da su duk da kokarin da suka yi wa jam’iyyar a 2019, barin jam’iyyar ba mafita bace.
“Mun fahimci takaicin da ku ke ciki kuma muna masu tabbatar muku da cewa zamu yi iyakar kokarin mu don kawo gyara da kuma hadin kan ‘yan jam’iyyar mu kafin zaben 2023.
“Don haka ina rokon wadanda suka bar jam’iyyar da su sauya tunani kuma su dawo asalin mazauninsu.”
Ya bukaci shugabannin APC na Jihar Kwara akan su taushi masu barin jam’iyyar
Ya tabbatar musu da cewa a tsaye yake don ganin ya kawo karshen rabuwar kawuna da kana ya kawo hadin kai ga jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kwara. Amma bai dace su fara tunanin barin jam’iyyar ba.
Gaba daya siyasarsa ya dage wurin kasancewa mai rikon amana kuma ba ya da burin sauyawa, a cewarsa.
Ya ce yana so ya yi amfani da wannan damar wurin kira ga shugabannin jam’iyyar akan su yi gaggawar ganin sun dakatar da ‘yan jam’iyyar da ke Kwara daga barin shekarsu.
2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari
A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.
Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.
Asali: Legit.ng