2023: Atiku,Wike da sauransu za su san makomarsu, kwamitin tsarin karba-karba na PDP zai zartar da hukunci yau

2023: Atiku,Wike da sauransu za su san makomarsu, kwamitin tsarin karba-karba na PDP zai zartar da hukunci yau

  • Ana sanya ran babbar jam’iyyar adawar kasar ta PDP za ta yanke hukunci kan yadda za ta yi rabon mukamai ga shiyya nan da yan awanni
  • Sakamakon haka, masu takara da dama sun bude kunnuwa don jin yadda hukuncin zai kaya domin shine zai nuna makomar kudirinsu
  • A halin da ake ciki, wasu daga cikin masu takarar sun sha alwashin ci gaba da tuntubar da suka fara

Ana sanya ran kwamitin tsarin karba-karba sna jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mambobi 37 zai sanar da hukuncinsa kan tsarin rabon shiyya-shiyya na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Kwamitin ya shirya yin watsi da tsarin karba-karba na jam’iyyar domin ba masu takarar shugaban kasarta damar fafatawa don mallakar tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani da za a yi a ranakun 28-29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

2023: Atiku, Wike da sauransu za su san makomarsu a yau yayin da kwamitin shiyya na PDP zai zartar da hukunci
2023: Atiku, Wike da sauransu za su san makomarsu a yau yayin da kwamitin shiyya na PDP zai zartar da hukunci Hoto: The Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Masu takarar kujerar shugaban kasa suna ta tuntuba da kamun kafa domin tabbatar da ganin cewa hukuncin da kwamitin zai dauka bai kawo masu cikas ba.

Wata majiya ta kusa da daya daga cikin masu takarar ya sanar da jaridar Daily Trust cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna jiran sakamakon kwamitin, amma ba zai hana mu tuntubarmu ba. Abune da za a ci gaba. Duk yadda sakamakon hukuncin kwamitin ya zo, za mu gani bayan nan.
“Amma dai a yanzu muna ci gaba da harkokinmu na yau da kullun. Mun san cewa kwamitin na da ra’ayin jam’iyyar a zuciyarsa.”

Wata majiya a jam’iyyar da ke kusa da daya daga cikin yan takarar da ke kokarin fitar da dan takarar yarjejeniya ta fada ma Daily Trust cewa:

“Ba za mu iya cewa komai ba a yanzu har sai kwamitin ya fito da hukuncinsa.

Kara karanta wannan

Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

“Ba ma so mu wuce gona da iri; tuni muka fara aiki kan tsarin yarjejeniya. Duk hukuncin da jam’iyyar ta zo da shi za mu daura daga nan.”

Saraki, Tambuwal, Mohammed sun kulla yarjejeniya kan wanda zai zama mataimakin shugaban kasa a 2023

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun yi wata ganawar sirri da Gwamna Ifeanyi Okowa.

Jiga-jigan kuma masu neman takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bukaci Okowa da ya nemi takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023.

Jaridar The Guardian ta rahoto daga wata majiya cewa a wajen taron wanda ya shafe tsawon wasu awowi, yan siyasar sun ce Okowa ya cancanci ayi aiki tare da shi saboda tarin kwarewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng