Minista Abubakar Malami ya bayyana kudirinsa na takarar gwamna, yace ba zai ci amana ba
- Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ya ayyana shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi
- Ministan wanda ya faɗi kudirinsa a gaban taron magoya bayansa, ya ɗauki alƙawarin cewa ba zai ci amana ba
- Tun a shekarar 2014, Ministan ya nemi takarar gwamna a APC, amma ya sha kaye a zaɓen fidda gwani
Kebbi - Ministan shari'a kuma Antoni Janar na ƙasar nan, Abubakar Malami, ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan Kebbi a babban zaɓen 2023 dake tafe.
This Day ta rahoto cewa Malami, wanda ya bayyana shirinsa a gaban dandazon masoyansa, ya ɗauki alƙawarin ba zai ci amanarsu ba.
A wani Bidiyo da ya watsu ranar Litinin, Ministan ya ce:
"Idan Allah mai girma da ɗaukaka ya so, kuma komai ya tafi dai-dai, zan nemi kujerar gwamnan jihar Kebbi, ina rokon goyon bayanku."
"Ina mai sanar da cewa zan nemi takara kuma bisa haka ina barar Addu'o'in ku da goyon baya domin ta haka ne zamu yi aiki tare kuma mu samu nasara a tseren."
"Bani da tarihin cin amana kuma ba zan ci amanar ku ba mutane na, zan muku aiki iyakar karfi na."
Zamu bauta wa Mutane - Malami
Malami, SAN, ya bayyana cewa shugabanni na bukatar magoya baya, haka nan magoya baya na bukatar shugabanni su tabbatar mutane sun amfana da jagorancin su.
Bugu da kari, ya lashi takobin yin aiki ba dare ba rana domin tabbatar da ya canza rayuwar al'ummar jihar Kebbi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A baya dai, wasu rahotanni sun nuna cewa Malami ya shaida wa abokansa na kusa cewa yana kwaɗayin shiga zaɓen jihar Kebbi.
Babu tantama zai nemi takara ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC kuma zai nemi ya ɗora daga inda gwamna Atiku Bagudu ya tsaya, wanda zai kammala zango na biyu.
A 2014, Malami ya sayi Fam ɗin sha'awar takara, amma ya sha ƙasa a hannun gwamna mai ci, Atiku Bagudu, tun a zaɓen fidda gwani.
A wani labarin kuma mai kama da wannan, Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya ayyana shiga tseren takara a zaɓen 2023
A wurin bikin karin shekara, tsohon shugaban APC na ƙasa ya ayyana shiga takarar kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa.
Kwamaret Adams Oshiomhole, ya ce lokaci ya yi da zai amsa kiran da mutane ke masa na ya wakilce su a majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng