Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya shiga tseren takarar Sanata a 2023

Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya shiga tseren takarar Sanata a 2023

  • A wurin bikin karin shekara, tsohon shugaban APC na ƙasa ya ayyana shiga takarar kujerar Sanata a zaɓe mai zuwa
  • Kwamaret Adams Oshiomhole, ya ce lokaci ya yi da zai amsa kiran da mutane ke masa na ya wakilce su a majalisar dattawa
  • A cewarsa, ko a baya rikicin da ya baibaye APC ne ya hana shi yanke hukunci, to amma yanzun komai ya wuce

Edo - Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana kudirinsa na wakiltar mazaɓar Edo ta arewa a majalisar dattawan Najeriya.

Oshiomhole ya ayyana haka ne a wurin bikin cikarsa shekara 70 a duniya wanda ya gudana a mahaifarsa Iyamho, ƙaramar hukumar Etsako West, jihar Edo, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari a ayyana shiga tseren kujerar gwamna a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba

A baya shugabannin APC na kananan hukumomi da gundumomi sun roke shi da ya wakilci mazaɓar a majalisar dattawan ƙasar nan.

Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole.
Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya shiga tseren takarar Sanata a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto Oshiomhole ya ce:

"Na faɗa a baya cewa matukar ba'a gyara APC ba, bai kamata mu yi maganar shiga zaɓe ba. Na rike kujerar Ciyaman na jam'iyya, na san hatsarin da ake fuskanta idan ba'a gyara ba."
"Kuma komai ya zo ƙarshe tun daga ranar 25 ga watan Maris, 2022, tare da zaɓan kwamitin ayyuka da majalisar ƙoli karkashin jagorancin tsohon gwamna, tsohon minista kuma Sanata mai ci, Adamu Abdullahi."
"Mutane na ta roko na, mai zai sa ba zan nemi kujerar Sanata ba? Ina amsawa da cewa farko dai rikicin APC, a bari mu shawo kan rikicin daga nan sai mu tattauna."

Kara karanta wannan

Gwamnan Adamawa ya faɗi sunan wanda PDP zata tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

Lokaci ya yi da zan fito takara - Adams

Oshiomhole ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za'a matsa zuwa mataki na gaba a lamarin wakilcin Edo ta arewa a majalisar tarayya daga 2023.

"Kuma lokaci ya yi da zan shiga tseren wakiltar Edo ta arewa a majalisar dattawa. Ina cigaba da jaraba kaina domin ba zan je majalisa na zauna, na saurari kudirori kuma duk karshen wata na karɓi Albashi ba."

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi barazanar maka PDP a Kotu kan kuɗin Fam

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin PDP, Ayoola Falola, ya koka kan yadda jam'iyya ta cika kuɗin Fam ɗinta.

Mista Falola ya yi zargin cewa miliyan N40m da PDP ta sanya ya yi yawa duba da halin ƙaƙanikayi da ake ciki a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262