Atiku ne zai karɓi tutar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Gwamna Fintiri
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahamdu Umaru Fintiru, ya ce Atiku ne zai karbi tutar PDP ta takarar kujerar shugaban ƙasa
- Gwamnan ya bayyana cewa Atiku ne ya dace ya jagoranci Najeriya kuma ya kammala duk wani shirin nasara a zaben fidda gwani
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na ɗaya daga cikin yan takarar da ke yunkurin samun tikitin PDP
Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai lashe tutar takara ta PDP a zaɓen 2023.
Gwamna Fintiri wanda ya nuna tabbacin nasarar Atiku, ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a filin jirgin ƙasa da ƙasa na Yola da daren ranar Lahadi.
Tribune Online ta rahoto cewa wannan shi ne karo na farko da gwamnan ya koma cikin jiharsa tun bayan da Atiku ya ayyana shiga takara.
Ahmadu Fintiri, ya ƙara da cewa Atiku Abubakar ne ɗaya tilo da zai iya karɓan tikitin jam'iyya a dai-dai irin wannan lokacin da ake ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane shiri Atiku yake yi?
Gwamnan Adamawan ya bayyana cewa tuni Atiku ya gama duk wasu shirye-shiryen haɗo kan magoya baya domin tabbatar da ya cimma burinsa na zama ɗan takaran PDP.
The Nation ta rahoto Ya ce:
"Kowace siyasa akan fara ta ne daga tushe, kowace kujera kake da buri, ƙarama ko mafi kololuwa dole ka kafa sansaninka a gida."
"Bisa haka, mu a Adamawa da sauran masu faɗa aji muna tare da jagoran mu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, da burinsa na zama shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023."
"Mun fara tsare-tsare, aiki ba kama hannun yaro, haka kuma muna kan aikin tattara magoya baya domin tabbatar wa Atiku ya zama mai kare tambarin PDP a Zaɓe.
Bugu da ƙari, gwamna Fintiri ya yi ikirarin cewa idan Atiku ya zama shugaban ƙasa zai haɗa kan Najeriya, daga lokacin lamarin tsaro ya zama tarihi.
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya yi barazanar maka PDP a Kotu kan kuɗin Fam
Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin PDP, Ayoola Falola, ya koka kan yadda jam'iyya ta cika kuɗin Fam ɗinta.
Mista Falola ya yi zargin cewa miliyan N40m da PDP ta sanya ya yi yawa duba da halin ƙaƙanikayi da ake ciki a ƙasa.
Asali: Legit.ng