Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro
- ‘Yan Majalisa sun dauki tsawon lokaci su na magana a kan lamarin rashin tsaro a zaman su na jiya
- Har ta kai wasu ‘Yan APC a majalisar wakilan sun fito su na sukar gwamnatin Muhammadu Buhari
- Hon. Aminu Suleiman ya bada shawarar rufe majalisa domin shugaban kasa ya yi abin da ya dace
Abuja - Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya sun kawo shawarar a rufe majalisar kasar gaba daya saboda shugaban kasa ya yi abin da ya dace.
Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris 2022. Hakan na zuwa ne bayan kashe-kashen da ake ta yi a fadin jihohin kasar nan.
‘Yan majalisar tarayyar su na ganin wannan zai iya sa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi-tsaye domin ya kare dukiya da kuma rayukan al’ummar Najeriya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wani ‘dan majalisar ya ke cewa ya kamata a tsige Babagana Monguno da hafsun sojin da aka nada a shekarar bara.
Rahoton ya ce ‘yan majalisa sun tashi aiki da wuri a ranar Alhamis ganin tattaunawar da ake yi a zauren ta dauki wata hanyar, kowa na aman abin da ke ransa.
Ba a iya yin zama a kan abin da ya kawo ‘yan majalisa a jiya ba, sai aka buge da sukar gwamnati.
'Yan APC sun caccaki gwamnatinsu
Mafi yawan wadanda suka yi ta Allah-wadai da gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma jami’an tsaron Najeriya, ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne masu rinjaye.
‘Ya ‘yan APC sun dauki fiye da sa’a guda su na caccakar gwamnati a kan batun tsaro. Hon. Shehu Balarabe ya kawo maganar kashe-kashen da ake yi a Kaduna.
An rahoto Hon. Aminu Suleiman ya na cewa abin ya fara fin karfin jami’an tsaro. ‘Dan majalisar tarayyar ya ce gwamnatin tarayya ta gaza kare al’ummar Arewa.
Hon. Suleiman shi ne ya bada shawarar ‘yan majalisar su rufe majalisa idan ba za a ji maganarsu ba.
“Idan matakan da mu ka dauka ba za su yi aiki ba, zai gagara ne a rufe majalisar nan, mu bi sahun ASUU, mu ce ba zamu koma bakin aiki ba?
“Har sai Mai girma shugaban kasa ya sauke nauyin da ke kan shi. Ba zarginsa na ke yi ba, amma a karshe, shi ne yake da ikon yin komai.”
- Hon. Aminu Suleiman
Ya kamata kowa ya samu makami?
An ji cewa Alhassan Ado-Doguwa ya koka, ya ce babban nauyin da ya rataya a kan gwamnati shi ne tsaro. ‘Dan majalisar ya ce ta kai ba za su iya wanke gwamnati ba.
Shi ma tsohon Sanatan nan, Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ba 'yan Najeriya 'yancin mallakar makami domin su iya kare kansu daga 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng