PDP ta samu gagarumin koma baya a Osun, Ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

PDP ta samu gagarumin koma baya a Osun, Ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

  • Ɗan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar Osun ya yi murabus daga kasancewarsa mamba
  • Dakta Akin Ogunbiyi, jigo a PDP reshen Osun ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyya na ƙasa
  • Ogunbiyi ya fusata tun kafin fara fafatawa a zaben fidda gwani kuma ya sanar da janye wa awanni kafin bisa wasu dalilai

Osun - Tsohon ɗan takarar gwamna kuma babban jigo a jam'iyyar hamayya PDP reshen Osun, Dr Akin Ogunbiyi, ya tsame kansa daga cikin jam'iyyar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Mista Ogunbiyi, ya sanar da matakin da ya ɗauka na barin PDP a wata wasikar murabus da ya aike wa shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Zan janye daga takarar shugaban ƙasa bisa sharaɗi ɗaya, Gwamnan dake mafarkin gaje Buhari a 2023

Tsohon ɗan takarar gwamnan Osun, Akin Ogunbiyi.
PDP ta samu gagarumin koma baya a Osun, Ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A cikin wasikar ta murabus, jigon PDP ya gode wa jam'iyya da mambobinta bisa, "Damawa da shi da kuma sauran harkoki na tsawon shekaru."

Tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dan Allah ka amince da wannan wasiƙa a matsayin murabus ɗina daga jam'iyyar PDP a hukumance daga ranar 28 ga watan Maris, 2022."

Abubuwan da suka faru kafin haka

Idan zaku iya tunawa, awanni kaɗan kafin fafata zaɓen fidda gwamni na ɗan takarar gwamna karkashin PDP, Dakta Ogunbiyi, ya sanar da janye wa daga cikin masu tseren tikiti.

Babban jigon PDP ya bayyana matsayarsa ne a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Ogo Oluwa, yankin Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Da yake faɗin dalilin janyewarsa daga tseren, ya bayyana cewa ya gano akwai wata maƙarƙashiya da aka ƙulla tun daga Hedkwatar jam'iyya ta ƙasa na yin murɗiya a zaɓen.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa kowace rana ake ƙara samun zaman lafiya a Najeriya, Gwamnatin Buhari ta magantu

Bugu da ƙari, ya ce tsagin Adeleke sun shirya murɗiya, cin mutunci da kuma ta da yamutsin da ka iya jawo rasa rayukan wasu masoyansa a wurin zaɓen.

A wani labarin kuma Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa

Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya kammala aikinsa ya mika ragamar tafiyar da APC hannun sabon shugaba.

Sanata Abdullahi Adamu, ya karɓi jagorancin APC a Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262