Tun kafin a je ko ina, PDP ta samu kusan Naira miliyan 300 daga saida fam din takara
- Kudin da jam’iyyar PDP ta ke samu daga saida fam din shiga takarar shugaban kasa ya na ta kara yawa
- A zaben na 2023, jam’iyyar hamayyar ta yi wa takardar neman tikitin shugaban kasa kudi a kan N40m
- Mutane bakwai da suka yanki fam sun yi sanadiyyar da jam’iyyar adawar ta samu Naira miliyan 280
Abuja - Akalla Naira miliyan 285 su ka shigo hannun jam’iyyar hamayya ta PDP daga wajen ‘yan takara takwas da su ke sha’awar takarar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta ce daga lokacin da majalisar NEC ta PDP ta amince a soma saida fam zuwa yanzu, har an samu kudin da ya haura Naira miliyan 200.
Zuwa ranar Talatar nan (29 ga watan Maris 2022), abin da aka tara daga mutanen da suke neman a ba su tutan jam’iyyar hamayyar shi ne Naira miliyan 280.
Maza bakwai da suka kwallafa rai a kan samun tikitin jam’iyyar PDP sun saye fam dinsu a kan Naira miliyan 40. Sai wata mace ta biya Naira miliyan biyar.
An yi wa mata da matasan da za su saye fam a jam’iyyar PDP rangwame saboda a rika yi da su.
Su wanene su ka saye fam?
‘Yan siyasan da suka saye fam ko kuma aka saya da sunansu, sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya yi takara a 2019.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi, Bala A. Mohammed.
Dr. Bukola Saraki da Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal sun saye wannan tikitin a zaben 2018.
Rahotanni sun ce ragowar wadanda suka biya makudan kudi suka saye fam din takarar su ne Anyim Pius Anyim, Dele Momodu da Nwachukwu Anakwenze.
Har zuwa wannan lokaci, Diana Oliver Tariela ce mace guda da ta saye fam a jam’iyyar ta PDP.
Da ya yanki na shi fam din, Dr. Nwachukwu Anakwenze ya bayyana cewa ya fi duk sauran ‘yan takarar da suka biya kudin shiga takara cancanta da dacewa.
Shawarar Anyim Pius Anyim
Ana da labari cewa Sanata Anyim Pius Anyim ya na da ra'ayin ba zai yiwu a iya cin zaben 2023 a kasar nan idan ‘dan takarar jam’iyyar PDP ya fito daga Arewa.
Babban ‘Dan siyasar ya ziyarci Arewacin Najeriya a makon nan a yunkurin da yake yi na ganin shi aka ba tikitin PDP, ya bada shawara a bi tsarin karba-karba.
Asali: Legit.ng