Shekara 1 da komawa APC, an dauki mukami mai tsoka, an damkawa tsohon ‘Dan adawa

Shekara 1 da komawa APC, an dauki mukami mai tsoka, an damkawa tsohon ‘Dan adawa

  • Sanata Iyiola Omisore daga jihar Osun ne ya zama sabon jam’iyyar APC mai mulki na kasa a NWC
  • Har zuwa bayan zaben 2019, Iyiola Omisore yana tare da jam’iyyar adawa, bai shiga APC ba tukun
  • Shekara guda da sauya-shekar tsohon mataimakin gwamnan na Osun, sai ya samu babbar kujera

Abuja – Jaridar Punch ta ce watanni 13 kenan da shigar Sanata Iyiola Omisore jam’iyyar APC mai mulki, sai ga shi ya zama sakataren jam’iyya na kasa.

Iyiola Omisore yana cikin sababbin shugabannin da aka zaba a APC ba tare da hamayya ba.

Hakan na nufin tsohon Sanatan na jihar Osun da sauran mutum fiye da 70 da aka zaba, za su rike majalisar aiwatarwa ta NWC a matakin APC na kasa.

Ga wadanda ba su sani ba, a 2002 ne aka shigar da karar Iyiola Omisore bisa zarginsa da aka yi da hannu wajen kisan tsohon Ministan shari’a, Bola Ige.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Daga baya kotu ta wanke sabon sakataren na APC da duk sauran wadanda aka shigar da kararsu.

Jaridar ta ce a shekarar 2016 hukumar EFCC ta cafke Omisore, ta zarge shi da karbar Naira biliyan 1.3 daga hannun Sambo Dasuki a lokacin shi ne NSA.

Manyan APC
Oyegun, Omisore, Aregbesole da Tinubu Hoto: pmnewsnigeria.com

Karatu da siyasar Omisore

An haifi Iyiola Omisore ne a garin Ondo , inda a nan ya tashi, har ya yi makarantar sakandare. Omisore ya yi digirin farko har zuwa PhD a Ingila da Faransa.

A 1999 ne ‘dan siyasar ya zama mataimakin gwamna a jihar Osun. Bayan nan ya zama Sanata. Daga baya ya nemi takarar gwamna a AD, PDP da kuma SDP.

Omisore ya shigo APC a 2021

A farkon 2021 ne Omisore ya shigo jam’iyyar APC mai mulki. Bayan watanni 13 da sauya-shekarsa, sai aka ji an zabe shi a matsayin sakatare na kasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Abba Gida-Gida ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

Fadar Shugaban kasa ta yi martani

Daily Trust ta rahoto cewa fadar shugaban kasa ta fitar da jawabi ta bakin Garba Shehu ta na cewa abin da ya ragewa APC shi ne a shirya zaben fitar da gwani.

Malam Shehu ya yi magana ne bayan jin jama’a su na surutun cewa tsofaffin ‘yan PDP aka damkawa mukamai a APC, ya ce ko a addini ana yafewa masu laifi.

“Shin littatafan addini ba su sanar da mu falalar tubabbun da suka tuba, suka canza halinsu ba.” - Malam Garba Shehu

Zaben APC na kasa

Ku na da labari cewa an fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a matakin APC na kasa, kuma babu wasu daga cikin ‘Yan takarar shugaba Muhammadu Buhari.

Abubakar Kyari ne ya zama mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa, a yankin Kudu kuwa aka zabi Emma Eneukwu a maimakon Farouk Adamu Aliyu da Ken Nnamani.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng