Kai Tsaye: Sakamakon zabe sabbin shugabannin APC na ƙasa ya fara bayyana

Kai Tsaye: Sakamakon zabe sabbin shugabannin APC na ƙasa ya fara bayyana

Jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da babban taronta na kasa a yau Asabar a Abuja.

Za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa da na shiyya a babban taron da za a gabatar a ranar 26 ga watan Fabrairu amma aka mayar ranar 26 ga Maris.

Wakilai 7,584 daga jihohi 36 na kasa da babban birnin tarayya Abuja ake sa ran za su halarci taron, shafin jamiyyar na Twitter ya tabbatar.

Wakilan za su zabi mambobi 22 na kwamitin ayyuka na kasa (NWC) daga cikin masu neman mukamai daban-daban 169 da za su karbi ragamar shugabancin jam’iyyar daga CECPC.

Jarin sunayen wadanda suka yi nasara da kuma mukamansu a taron APC

  1. Sanata Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa shine sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.
  2. F.N. Nwosu ya bayyana a matsayin sakataren walwala na kasa na jam’iyyar APC
  3. Suleiman Muhammad Argungu daga jihar Kebbi shine sabon sakataren shirye-shiryen APC na kasa
  4. Felix Morka shine sabon sakataren yada labaran APC na kasa
  5. Sanata Iyiola Omisore daga jihar Osun (kudu maso yamma) shine sabon sakataren APC na kasa.
  6. Betta Edu, kwamishinar Cross River, ita ce shugabar mata ta kasa bayan ta samu kuri'u 2,063.
  7. Mustapha Salihu ya bayyana wanda ya lashe kujerar mataimakin shugaban kasa (arewa maso gabas)

Osinbajo yana saka kuria ya bar dandalin Eagle Sqaure

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayin da yake saka kuria a dandalin Eagle Sqaure, yana kammalawa ya bar wurin taron

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Ta tabbata, Abdullahi Adamu ya zama shugaban APC

An sanar da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC.

Wannan ya biyo bayan janye masa dukkan sauran takaran sukayi bisa bukatar shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Buhari ya isa wajen taron

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira wajen taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da ake yi a Eagle Square a Abuja.

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya saki bidiyon lokacin da shugaban kasan ya isa farfajiyar.

Ya isa wajen misalin karfe 8.25 na dare.

Da duminsa: Yakubu Dogara ya janye daga takarar mataimakin shugaban APC na kasa

Yakubu Dogara ya janye daga takarar mataimakin shugaban APC na kasa

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Gwwamnoni 5 na APC daga kudu maso yamma sun fitar da sunayen yan takaran hadin kai

Gwamnonin APC biyar a yankin Kudu-maso-Yamma sun amince da fitar da takardar da ta kunshi sunayen wadanda za a zaba daga yankin su a babban taron jam’iyyar na kasa da ke gudana a Abuja.

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa Hoto daga Leadership
Asali: Facebook

Bidiyon Sanata Adamu yayin da yake kwasar rawa cike da farin ciki tare da Al Makura

Bidiyon Sanata Abdullahi Adamu yayin da yake kwasar rawa ciki da farin ciki tare da Sanata Al Makura bayan ya janye daga cikin yan takara tare da bayyana goyon bayansa garesa.

Gwamna Sule da FFK yayin da suka zagaya Eagle Square

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa tare da Femi Fani-Kayode yayin da suke zagaye dandalin Eagle Square dake Abuja

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Sanata Okorocha ya isa wurin taron gangamin APC na kasa

Okorocha ya isa dandalin Eagle Square wurin taron gangamin APC na kasa

Sanatan Imo ta yamma, Rochas Okorocha ya isa wurin taron da ake yi wanda ya cika dankam a Abuja.

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamna Yahaya Bello tare da tawagarsa sun dira filin Eagle Square wurin taron gangamin APC

Gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar shugabancin kasar Najeriya karkashin inuwar APC, Yahaya Bello, ya isa dandalin Eagle Square wurin taron gangamin zaben shugabannin APC na kasa da yankuna.

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

Taro ya yo taro, hatta nakasassu sun samu shiga dandalin Eagle Square

Mutane masu nakasa suna samun hanyar shiga dandalin Eagle Square duk da matsalolin da wakilai ke fuskanta don samun damar shiga.

An fara tantance wakilan jamiyya a dandalin Eagle Square kafin kada kuria

Bayanai da ke zuwa a halin yanzu shine na fara tantance wakilan jamiyya a dandalin Eagle Square kafin a fara kada kuriar zabe

Taron APC: An tsaurara matakan tsaro a kewayen Eagle Square, kofar shiga 1 ce a bude

Kofa daya kacal aka bude wa wakilai da ‘yan jarida yayin da dubbai ke fafutukar ganin sun shiga filin taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a dandalin Eagle Square a ranar Asabar 26 ga watan Maris.

Fastocin Tinubu, Osinbajo, Umahi, Bello da sauransu sun mamaye dandalin Eagle Square

Abin da ya kamata ya zama babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a dandalin Eagles Square, Abuja, a ranar Asabar, 26 ga watan Maris, ya rikide zuwa gagarumin wurin yakin neman zabe na magoya bayan masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Hotunan yakin neman zaben mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Gwamna Dave Umahi, Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Yahaya Bello da Gwamna Abdullahi Ganduje sun mamaye filin wasan.

Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Kai Tsaye: Yadda ake fafatawa a Eagle Square yayin zaben sabbin shugabannin APC na ƙasa
Asali: Original

Kwamitin zabe na APC ya isa dandalin Eagle Square

Kwamitin zabe na babban taron jam’iyyar APC na kasa ya isa dandalin Eagle Square da ke wurin da za a gudanar da babban taron a Abuja.

Wakilan kwamitin sun shigo wurin da kayan zabe, duk da cewa shugabansu, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufai, baya tare da su.

Al-Makura Ya Janye Daga Takarar Shugabancin APC, Ya Goyi Bayan Adamu

Al-Makura ya janye daga takarar shugabancin APC, ya goyi bayan Adamu a matsayin dan takarar yarjejeniya

Dan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Sanata Umaru Tanko Al-Makura ya janye daga takarar, kamar yadda kakakinsa, Danjuma Joseph ya tabbatar.

Sanata Al-Makura, tsohon gwamnan jihar Nasarawa wanda a halin yanzu yake wakiltar Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da wannan ‘yan sa’o’i kadan kafin taron da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 26 ga Maris, 2022 a Abuja. Ya yi alkawarin marawa Sanata Abdullahi Adamu baya.

Online view pixel