Mu muka kashe Najeriya, dole tare mu zamu gyara: Bola Tinubu

Mu muka kashe Najeriya, dole tare mu zamu gyara: Bola Tinubu

  • Jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata yan Najeriya su fadawa juna gaskiya
  • Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana niyyar takarar kujeran shugaban kasa a zaben Febrairun 2023
  • Tinubu ya bada kyautar cibiyar karatu na kimanin kudi biliyan daya ga jami'ar jihar Legas LASU

Legas - Mai niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa dukkanmu muka kashe Najeriya kuma mu zamu iya gyarata.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a lakcan bikin yaye daliban jami'ar jihar Legas LASU.

Ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr Obafemi Hamzat, rahoton Vanguard.

Bola Tinubu
Mu muka kashe Najeriya, dole tare mu zamu gyara: Bola Tinubu Hoto: Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Atiku, Ribadu, Tambuwal, da wadanda suka yafe neman Shugaban kasa, su ka nemi Gwamna

Yace:

"Mu daina yaudarar kawunanmu. Mun dade muna ikirarin cewa muna da arziki kuma gobe zamu ji dadi amma shekaru na taf
iya kuma babu cigaba."
"Da fadin cigaba a baki zai kawo cigaba, da mun kasance kasa mafi cigaba a duniya."
"Amma kash, Najeriya na waje guda. Mun zama masu fitar da dukiyarmu amma mu shigo da kaya da tsada."
"Wajibi ne mu fadawa juna gaskiya, mu fuskancesa mu gyara. Dukkan mu muka janyo kuma zamu iya zama mafita. Mu hada kai. Wajibi ne mu gyara kasar nan."

A kan rashin aikin yin matasa, Tinubu ya ce rashin aiki da aiki babu albashin kwarai tsakanin matasa ya kai 60%, kuma wajibi ne a magance hakan.

Tinubu yace samawa matashin birane aikin yi, aikin noma, harkar gidaje, ilimi, tattalin arziki da manyan ayyuka ya kamata gwamnati ta mayar da hankali.

Tinubu ya bada kyautar cibiyar karatu na kimanin kudi biliyan daya ga makarantar.

Kara karanta wannan

Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai farfado da tattalin arzikin Najeriya tare da rage dogaro kan arzikin man fetur.

Dan takaran kujeran shugaban kasan ya ce ya yi niyyar gadar kujerar shugaba Muhammadu Buhari ne don amfanin yan Najeriya.

Tinubu yace rashin wutar lantarki ne babban matsala ga cigaban tattalin arzikin Najeriya saboda rashin wuta ke kara farashin kaya, hana mutane aiki cikin nishadi, da kuma kawo tasku ga samar da ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: