Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya sha alwashin dinke barakar da APC idan har ya zama shugaban jam'iyyar na kasa
  • Yari ya ce domin ganin ya cimma haka, zai yi amfani da gogewar da ya samu a matsayin dan majalisa da kuma gwamna
  • Dan siyasar na daya daga cikin mutane bakwai da ke takarar kujerar shugabancin jam'iyyar a babban taron da za a yi a ranar Asabar mai zuwa

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa zai yi amfani da gogewar da ya samu yayin da yake a matsayin dan majalisa da gwamna wajen saitawa da gyara jam’iyyar.

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Ya ce kwarewarsa a mukaman gwamnati da ya rike a baya ya koyar da shi abubuwa da dama kuma ya dora shi a kan hanya wajen sauke hakkokin da suka rataya a wuyansa.

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC
Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Yari wanda ya taba rike mukamin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya sannan ya riki mukamai daban-daban a rusasshiyar jam’iyyar All Nigerian Peoples Party (ANPP), ya ce ya san yadda ake tafiyar da jam’iyya.

Ya ce:

“Ya taimaka mani sosai musamman wajen ba da fifiko ga rabon kudade.
“Don haka, na koyi abubuwa da yawa, kuma hakan ya taimaka mani sosai a wajen shugabanci, wajen tafiyar da mulkin jihar.
“Na san yadda ake hulda a ciki da wajen jam’iyyar kuma zan iya aiki tare da kowannenku don ci gaban jam’iyyartmu da na kanmu.”

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdulaziz Yari

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 nake son cimmawa idan na gaji El-Rufai

A gefe guda, Abdulaziz Yari ya ayyana cewa karba-karba ya saba kundin tsarin mulki a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yari ya kuma bayyana cewa shi ya riga ya siya fom din takarar kujerar shugaban jam’iyyar gabannin babban taron ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Leadership ta rahoto cewa Yari wanda ya bayyana hakan yayin da ya gana da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar dattawa da kuma neman goyon bayansu, ya ce ya zama dole jam’iyyar ta samar da wanda zai iya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng