Babu inda aka yi wata yarjejeniyar mikawa Yarbawa mulki bayan 2023 inji kusoshin APC

Babu inda aka yi wata yarjejeniyar mikawa Yarbawa mulki bayan 2023 inji kusoshin APC

  • Akwai masu tunanin an yi alkawari shugabanci zai koma bangaren kudu maso yamma a zaben 2023
  • Wasu manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun nuna sam babu inda aka taba yi wannan maganar
  • Ko ma da an taba yin wannan zancen, akwai wadanda ke ganin ba za ta yiwu a cika alkawarin ba

Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki sun yi watsi da rahoton da ke cewa akwai yarjejeniyar da aka yi na mika mulki zuwa kudu maso yamma.

Jaridar Vanguard ta fitar da wani labari da yake cewa kusoshin na APC sun nuna cewa ba a ajiye wannan alkawari a lokacin da aka kafa jam’iyyar APC a 2013 ba.

Wani cikin jiga-jigan APC wanda da su aka kafa jam’iyya ya ce babu wani abu makamacin damkawa kudu maso yamma mulki da aka yi magana kafin 2015.

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

“Babu wani abu mai kama da wannan da ya faru. Ba ayi wani zama ko makamancinsa a kan kai mulki zuwa kudu maso yamma ba.” - Wata majiya

Da kamar wahala

Haka zalika wani babba a jam’iyyar mai mulki ya shaidawa jaridar irin haka, ya ce da wahala a iya cewa Muhammadu Buhari zai bar magajinsa ya fito daga nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ko da an yi wannan alkawari a baya, babu tabbacin za a cika shi a zabe mai zuwa. Ya ce ba a san wa zai gaji Buhari ba, amma an sa wanene ba zai yi ba.

Buhari
Bola Tinubu da Shugaba Buhari Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

“Ba mu san wanene zai karbi mulki bayan shugaban kasa Buhari ba, amma mun san su wanene ba za su zama magadansa ba.” - Wata majiyar.

Zuwa yanzu, ‘dan siyasar bai yi karin haske ko fashin baki a kan wannan jawabin da ya yi ba.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Yamutsi a kan zaben APC

Rahoton ya ce baya ga batun samun takarar shugaban kasa, ana fama da sabani a jam’iyyar APC a dalilin yadda za a raba mukaman shugabannin APC na kasa.

Wasu ‘ya ‘yan APC a jihar Abia sun bayyana cewa ba su yarda a tsaida Henry Ikoh a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban APC na kudu maso gabas ba.

‘Yan takara uku ne daga kasar Yarbawa suke son zama sakararen APC. Bayan Iyiola Omisore, akwai Olaiya Abideen Olaitan, Adebayor Shitu da Ife Oyedele.

NNPP ta na tada kura

An ji 'Yan siyasa irinsu Bello Zaki da Hon. Rabiu Isa Taura, Hannafi Fagam, da Shehu Chamo sun bi Malam Aminu Ringim zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Jigawa.

Haka zalika Abdulaziz Usman Tarabu wanda ya rike kujerar majalisar wakilan tarayya da na dattawa tsakanin 1999 da 2007 ya bi NNPP mai kayan marmari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng