Wasu ‘Yan Arewa su na so Jonathan ya koma Aso Rock a 2023, za su ba shi fam kyauta

Wasu ‘Yan Arewa su na so Jonathan ya koma Aso Rock a 2023, za su ba shi fam kyauta

  • Shugaban kungiyar Middle Belt Progressive Forum ya ce su na goyon bayan Goodluck Jonathan
  • Dr. Paul Agada ya ce kungiyarsu za ta sayawa Dr. Jonathan fam a duk jam’iyyar da yake sha’awa
  • A ra’ayin Middle Belt Progressive Forum, Goodluck ne ya cancanta ya sake shugabantar Najeriya

Abuja - Kungiyar nan ta Middle Belt Progressive Forum ta yi alkawarin sayen fam din takara domin Goodluck Jonathan ya sake neman mulkin Najeriya.

Wani rahoto da ya fito daga jaridar The Cable a ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, ya bayyana cewa kungiyar tayi wa Dr. Goodluck Jonathan ne mubaya’a.

Middle Belt Progressive Forum za su yanki fam din takara a kowace jam’iyyar siyasa domin ganin tsohon shugaban na Najeriya ya kuma samun shugabancin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Kungiyar ta yi wannan bayani ne a ranar Talatar nan ta bakin shugabanta na kasa, Dr. Paul Agada.

Babu irin Jonathan - Agada

A wani jawabi da ya fitar, Agada ya yi ikirarin Jonathan ya na da wasu halaye na musamman wanda suka sa ya cancanci ya sake jagorantar ‘Yan Najeriya.

A cewar shugaban wannan kungiya ta mutanen Arewa maso tsakiya, a mulkin Jonathan, matasa sun samu aikin yi, kuma an bunkasa harkar gona a kasar nan.

Goodluck Ebele Jonathan
Goodluck Ebele Jonathan da Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Dr. Goodluck Jonathan ne mai son zaman lafiya wanda a baya ya nuna cewa ba zai musanya burinsa da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar nan ba.”
“Wannan wani hali ne da ba kowa ya mallaka ba, wanda ya sa ya yi suna a matsayin mai kawo zaman lafiya da kokarin yin sulhu a daukacin nahiyar Afrika.”

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Alheran gwamnatin Jonathan

An rahoto Agada yana cewa har yau ana tuna gwamnatin Jonathan saboda kirkiro jami’o’in tarayya a Lokoja da Lafia da su ke yankin Arewa maso tsakiya.

A gwamnatinsa ne kuma aka ware N30bn na tsarin SURE-P domin gina gadar Loko zuwa Oweto wanda ta hada Benuwai da Nasarawa, sai yanzu aka gama aikin.

Agada ya ce su na rokon Jonathan ya amsa kiran Middle Belt Progressive Forum da dinbin mutanen Najeriya da ke gida da kasar waje, ya fito neman takara.

Saraki na neman mulki

An ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi alkawari zai ba matasa kujerar Ministoci tun da suka sayo masa fam din PDP ba tare da aljihunsa ya yi ciwo ba.

Bukola Saraki ya ce idan ya samu mulki a 2023, to zai ba matasa duk wata kujerar karamar Minista, kuma dole zai rika tafiya da su a harkar gwamnatinsa a PDP.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Matasa sun yi karo-karo, sun lale N40m, sun sayawa Bukola Saraki fam a PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng