Allah ya amince jam'iyyar APC ta gudanar da babban taro na ƙasa, Gwamna ya faɗi wani sirri

Allah ya amince jam'iyyar APC ta gudanar da babban taro na ƙasa, Gwamna ya faɗi wani sirri

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya ce APC ta gama duk wani shiri na tabbatar da samun nasara a babban taro na ƙasa ranar Asabar
  • Gwamna ya ce duk me tunanin APC ba zata iya taron ta ranar 26 ga wata ba to ya koma ya canza shiri, domin Allah ya amince
  • Ya ce kowane bangare na taron da kwamitoci sun kama aiki ba ji ba gani dan haka taro zai gudana cikin nasara

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce jam'iyyar APC ta kammala duk wani shiri na gudanar da babban taro na ƙasa ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022.

Gwamnan ya ƙara da cewa tuni Allah ya amincewa APC ta gudanar da taron, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Uzodinma ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai na gidan gwamnati jim ƙaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC, Bawa, ya yi martani kan kamen tsohon gwamna, zargin cin zarafinsa a siyasance

Gwamna Hope Uzodinma na Imo
Allah ya amince jam'iyyar APC ta gudanar da babban taro na ƙasa, Gwamna ya faɗi wani sirri Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Ya ce ba gudu ba ja da baya game da babban gangamin taron APC na ƙasa domin kowane kwamiti na aiki ba dare ba rana domin cika aikin da aka ɗora masa cikin nasara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tambaye shi cewa da alamun ba za'a gudanar da taron APC ranar Asabar ba domin matakan da ya kamata ace an ɗauka har yanzun shiru kake ji, gwamnan ya ba da amsa da cewa:

"In dai game da taron APC ne, to ni bansan wane alamu kuke son gani da zasu tabbatar muku za'a yi shi ranar Asabar. Tun jiya Lahadi, kowane kwamiti ya duƙufa aikinsa."
"Kwamitin tantancewa da sauran su, ina da masaniyar duk sun kammala shirin su, jira kawai suke. An kammala shirya wurin taro."
"Na faɗa muku, APC ce mai nasara, dan haka sauran jam'iyyu ke Alla-Allah APC ta tarwatse ko ta rasa murya ɗaya. Amma duk da tunaninsu, APC ba zata saki abin da ke hannunta ba, saboda abin da muke da shi yardar mutum miliyan N200m."

Kara karanta wannan

2023: Kokarin sulhi ya tsaya cak, Jam'iyyar APC na kan siraɗin tarwatsewa, Sanata Goje ya magantu

Allah ya amince da taron APC - Hope

Gwamnan ya tabbatar da cewa APC zata gudanar da babban taro na ƙasa cikin nasara da kuma kwanciyar hankali ranar Asabar dake tafe, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

"Duk wani dake tunanin za'a samu matsala, yana bukatar yaje ya ƙara addu'a domin Allah ya riga ya amince da taron APC."

A wani labarin kuma Jerin sunayen tsofaffin gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta damƙe bayan tube musu rigar kariya

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama gwamnonin Najeriya da dama bayan tube musu rigar kariya.

A binciken da muka tattara hukumar ta yi ram da aƙalla tsofaffin gwamnoni 33 bisa tuhume-tuhume da suka shafi halasta kuɗin haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262