Tsohon gwamna Al-Makura: Ku bani shugabancin APC na mikar da ita hanya dodar
- Gwamnan jihar Nasarawa yace shi mutum daya ne zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar APC mai mulkin kasar
- Tanko Al-Makura ya ce yana da dukkan abubuwan da ake bukata domin jagorantar jam’iyya mai mulki, musamman ma wajen magance rikicin da take fuskanta
- Tsohon gwamnan ya yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar a jiharsa da su ci gaba da mara masa baya na neman zama shugaban jam’iyyar APC na kasa
Daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC ta kasa, Tanko Al-Makura, ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki.
Al-Makura wanda ya yi gwamnan a jihar Nasarawa a tsakanin 2011 zuwa 2019, ya ce yana da dukkan abin da ya kamata na jagorancin jam’iyyar APC domin gudanar da zaben 2023 cikin nasara.
PDP ta tausayawa matasa wajen biyan kudin fam din takara, ta rage masu 50% da wasu hukunci 11 da ta zartar
Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya yi takama da cewa shi kadai ne dan takarar shugabancin APC na kasa wanda ke da cikakken goyon bayan jiharsa.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa zai kawo karshen rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar da zarar ya zama shugabanta na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yan jihata kowa na goyon bayana, Al-Makura
Tsohon gwamnan a lokacin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar APC na majalisar wakilai a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, ya ce duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun amince da gogewarsa.
A kalamansa:
“Dukkan mutanen da aka zaba a Jihar Nasarawa sun amince da takara ta. Siyasar cikin gida. Daga kan gwamna har ’yan majalisar tarayya, da ‘yan majalisan jiha, kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da shugabannin jam’iyya duk sun amince da takara ta."
Al-Makura duk da cewa yana fafatawa ne da tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu - dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba - ya ce yana da dukkan kwarewar da ake bukata don daidaita jam'iyyar, rahoton Punch.
A cewar tsohon gwamnan, ya fara harkar siyasa tun yana dalibi, kuma tun daga lokacin da ya kammala karatunsa, harkar jagoranci yake yi.
Abubuwan da Gwamna Buni da Bello suka tattauna a ganawarsu
A wani labarin, gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja a ranar Juma'a ya ziyarci takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa (CECPC).
Idan baku manta ba, rahoton jaridar Tribune ya bayyana cewa, gwamna Buni da Bello sun shiga ganawa bayan dawowar Buni.
A cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu, ya ce Bello ya jagoranci sauran mambobin tawagar CECPC wajen tarbar Buni a dawowarsa gida daga jinyar da ya yi a Dubai, PM News ta ruwaito.
Asali: Legit.ng