'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023
- Matashi ɗan shekara 45 daga jihar Osun yace lokaci ya yi matasa zasu fito su karbi ragamar mulkin Najeriya
- Mista Joseph, wanda ya bayyana shiga tseren takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a 2023, ya ce ya shirya tsaf domin kawo canji
- A cewarsa iyaye sun yi an gani kuma sun gaza, dan haka zai dawo da kyakkyawan Sa Rai a zukatan yan kasa
Osun - Faduri Oluware Joseph, ɗan kimanin shekara 45 daga jihar Osun, a ranar Alhamis, ya bayyana sha'awar neman takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.
Daily Trust ta ce matashin ya faɗi haka a wurin taron manema labarai da ya gudana a Sakatariyar ƙungiyar yan jarida NUJ dake babban birnin tarayya Abuja.
Ɗan takarar a karkashin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, ya jaddada cewa ya shiga tseren ne domin dawo da kyakkyawan sa rai da fata a ƙasar nan.
A kalamansa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Zan dawo da sa rai ga yan Najeriyan da suke yanke tsammani, zan gina kyakkyawan fata a zukatan yan Najeriya na gida da kuma na waje, musamman waɗan da suka cire tsammani. Ƙasar mu zata kuma ɗaukaka."
Ya ƙara da cewa Najeriya zata gyaru bayan ta keta wasu shekaru na ƙaƙanikayi, domin akwai albarkatun da za'a cimma nasara.
"Babu tantama iyayen mu sun kunyata ƙasar nan kuma lokaci ya yi da zasu kauce su bamu wuri, sun tafiyar da harkoki amma sun gaza, yanzu lokacin mu ne matasa mu taso."
"Lokaci ya yi da zamu sadaukar domin ƙasar nan ta mu, wannan wahalar ta isa haka, mun gaji haka nan."
Ɗan takarar ya gargaɗi yan Najeriya game da 2023
Mista Joseph ya roki yan Najeriya su nuna wayewa, kada su bari wasu yan siyasa su yaudare su da wata kyauta da bata taka kara ta karya ba a zaɓen 2023.
"Ya kamata matasa mu yi karatun ta natsu, mun fita zanga-zanga kwararo-kwararo na tsawon lokaci kuma har yanzun abin da muke iyawa kenan."
"Dan haka lokaci ya yi, ba zamu cigaba da fita tituna zanga-zanga ba, amma da katin zaɓen mu PVC zamu zaɓi jagorori nagari."
"Ban taɓa zama ɗan siyasa ba kuma bana fatan zama, kawai ina son jagorantar mutane domin gyara ƙasar da take da komai, amma ba abin da ke tafiya dai-dai."
A wani labarin na daban kuma Kotun Musulunci a Kano Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Sheikh Abduljabbar
Babbar Kotun Musulunci a Kano dake sauraron karar Abduljabbar ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar ba da beli.
Alkalin Kotun ya sanya ranar 31 ga watan Maris, 2022 domin bayyana matsayar Kotu kan bukatar bayan sauraron ɓangarorin biyu.
Asali: Legit.ng