Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa

Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa

  • Tsohon dan majalisar wakilai, Yemi Arokodare ya bukaci yan Najeriya da su zabi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a matsayin shugaban kasa a 2023
  • Arokodare ya ce Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu
  • Ya kuma ce gwamnan na Sokoto zai kai kasar ga matakin ci gaba idan har aka bashi dama

Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai, Yemi Arokodare ya roki yan Najeriya da su baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal damar shugabantar kasar da kawo sauye-sauye don inganta kasar.

Arokodare, wanda ya kasance a majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007 kuma shugaban kwamitin majalisar kan labarai, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Aiki kai tsaye ga masu 1st Class: Majalisa ta tattauna kan daukar masu digiri aiki

Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa
Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ya ce:

“Tambuwal na da jajaircewar shugabanci, Kankan da kai da kuma juriya don sauya fasalin kasar, gyara ta da kuma ceto ta.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta kuma rahoto cewa ya roki jam’iyyar PDP da ta baiwa gwamnan na jihar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilan damar zama dan takararta.

A cewarsa:

“Gwamna Tambuwal ya yiwa majalisar wakilai jagoranci mai kyau, ya nuna adalci da daidaito a shugabancinsa; yakamata mu bashi dama domin ya gyara yardar da aka bata tsakanin arewa da kudu.
“Idan za mu iya ba Tambuwal gagarumin dama na shugabancin wannan kasa mai albarka wacce aka yiwa riko mara kyau, lallai mu kwana da sanin cewa wannan mutumin zai hada kan arewa da kudu domin gyara Najeriya.
“Ya taba jagorantar yan majalisa daga yankuna daban-daban na kasar, kuma ya nuna shugabanci nagari da ba a saba gani ba, wanda ya sanya shi a mizanin wanda zai iya jagorantar Najeriya bisa adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

“Najeriya na bukatar a sauya fasalin ta tare da sabbin shugabannin da aka gwada kuma aka aminta da su wadanda za su iya ciyar da kasar gaba, kuma Tambuwal mutum ne da za mu iya yarda da shi a kan hakan.
“Tambuwal ya jagoranci kungiyar gwamnonin PDP da kyau; ya yi alaka da shugabanni da ‘yan jam’iyyar cikin mutuntawa; shi ne irin shugaban da zai iya hada kan kasar.”

Gwamna Aminu Tambuwal ya ba matasa satar amsar wanda za su marawa baya a 2023

A gefe guda, mun ji cewa mai girma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ba matasan kasar nan shawarar su guji zaben tsoho ya zama shugaban kasa a 2023.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya hada da kungiyar daliban jami’an kasar nan. Premium Times ta kawo wannan rahoton.

Aminu Waziri Tambuwal ya hadu da shugabannin kungiyar NANS na duka reshen jihohin Arewacin Najeriya a jihar Jigawa, inda su ka yi masa mubaya’a.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng