Ubandoma: Atiku bai taba tafiyar neman lafiya Turai a boye ba
- Daraktan labarai na kungiyar AtikuKawai, Zayyan Ubandoma, ya karyata rade-radin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya saci jiki ya je jinya Jamus
- Ubandoma ya ce koda dai tsufa ba karya bane, Atiku na da lafiyar jiki da na kwakwalwa da zai iya shugabancin Najeriya
- Matar Atiku, Jennifer Douglas, me neman saki ce ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tafi Jamus ganin likita
Daraktan labarai na kungiyar AtikuKawai a yankin arewa maso tsakiya, Zayyan Ubandoma, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bai taba zuwa kasar Jamus ganin likita a boye ba.
Ubandoma ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a daren ranar Litinin, 14 ga watan Maris, PM News ta rahoto.
Hadimin labaran ya yi watsi da rahoton duk da sanar da shi da aka yi cewa matar Atiku ta hudu Jennifer Douglas, wacce ke neman saki ta bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tafi Jamus ganin likita.
Rahoton ya nakalto Ubandoma yana cewa:
“Karya ne!! Atiku bai taba zuwa Jamus yin kowani irin jinya ba. Gaskiya ne cewa tsufa halitta ce, amma Atiku na da lafiyar kwakwalwa da na jiki da zai iya shugabantar Najeriya don budewa matasa hanyar da za su samu damammaki.”
Da aka nemi sanin ko Atiku zai yi amfani da likitocin Najeriya da asibitin fadar gwamnati idan ya zama shugaban kasa, Ubandoma ya ce:
"Ka gani, yana bisa tarihi cewa Atiku da ahlinsa gaba daya suna samun kulawar likita ne a Najeriya. Dukkanin ‘ya’yansa sun yi karatu a waje sannan ya kan tabbatar da ganin cewa dukkansu sun dawo gida Najeriya kuma ya hana dukkaninsu zama a chan. Wannan ya kasance ne saboda ya yarda da Najeriya."
Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace
A wani labarin, mun kawo cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sanar da kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.
Ya bayyana kudirin nasa ne a ranar Talata, 15 ga watan Maris, yayin wata ganawa da shugabannin APC a Abuja, Channels tv ta rawaito.
Atiku wanda ya kasance dan takarar babbar jam’iyyar adawar a zaben 2019, ya roki a sake bashi dama domin ya wakilci PDP a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng