2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai
- Kwamishinan tsare-tsare da kasafin Kudi na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirinsa na gadar kujerar gwamna Nasir El-Rufai a 2023
- Dattijon da ba a dade da ba shi mukami ba a jami’ar kasuwanci ta Henly da ke Ingila ba, ya shaida hakan a ranar Talata a wata wallafar da ya yi a Facebook
- A cewarsa yanzu zai fara kamfen din neman kujerar gwamna kuma yana da yakinin cin nasara musamman idan mutane suka duba ayyukan da ya yi wa jihar
Jihar Kaduna - Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirin sa na maye gurbin Gwamna Nasir El-Rufai a 2023, The Punch ta ruwaito.
Dattijo, wanda makarantar kasuwanci ta Henley da ke Jami’ar Reading a Ingila ba ta dade da ba shi mukami ba a cibiyar Dunning Africa, ya shaida hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata.

Kara karanta wannan
2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Asali: Facebook
Kamar yadda ya bayyana:
“Na yi wannan wallafar ne don sanar da niyyata ta fara kamfen din neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 da ke karatowa.”
Ya ce zai dasa daga inda El-Rufai ya tsaya
Yayin yaba wa gwamnan akan ba shi damar yin aiki da gwamnatin sa, The Punch ta ruwaito yadda tsohon shugaban ma’aikatan jihar ya ci gaba da cewa:
“Tsawon shekaru bakwai da suka gabata, na samu damar yin aiki tare da gwamnan mu, uba kuma shugaba Nasir El-Rufai yayin kokarinsa na gyara jihar mu.
“Tun da aka kafa Jihar Kaduna a tarihi, ba a taba samun gyara irin wanda aka yi daga shekarar 2015 zuwa yanzu ba. Yayin da na samu damar yin ayyuka a manyan mukamai, daga shugaban ma’aikatan jihar zuwa kwamishina; na samu damar yin aiki tukuru don ciyar da jihar gaba.

Kara karanta wannan
Da Duminsa: Uba Sani ya bayyana kudurinsa na neman kujerar gwamnan Kaduna a APC a 2023
“Ina da yakini akan cewa zan iya yin aiki kwarai tare da samar ci gaba mara misaltuwa sannan in dasa daga inda Malam Nasir El-Rufai ya tsaya.”
Ya kara da cewa saboda gogewar sa, zai tabbatar ya yi aiki komai wuya komai rintsi don tallafa wa Jihar Kaduna.
Hakan yasa ya ce yana so a ba shi damar yin aiki kwatankwacin wanda mutanen Kaduna suka gani a shekaru 7 da suka gabata.
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Asali: Legit.ng