An tunawa ‘Yar Abiola abin da ta fada a 2018 a kan APC yayin da ta shirya tsayawa takara

An tunawa ‘Yar Abiola abin da ta fada a 2018 a kan APC yayin da ta shirya tsayawa takara

  • Rinsola Abiola ta bayyana shirinta na zama shugabar matasa ta jam’iyyar APC na kasa baki daya
  • ‘Diyar Marigayi MKO Abiola za ta nemi wannan mukamin ne tun da an kai kujerar zuwa yankinta
  • Tsohuwar hadimar ta Hon. Yakubu Dogara ta taba zargin jam’iyyar APC da rashin daraja matasa

Bisa dukkan alamu za a gwabza wajen neman kujerar shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa a zaben shugabanni na kasa da za a gudanar a Maris.

Rinsola Abiola ta bayyana cewa za ta tsaya neman shugaban matasan jam’iyyar APC, ganin an kai kujerar zuwa yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Rinsola Abiola ta fito ta shaidawa Duniya matsayar da ta dauka ne a Twitter a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris 2022.

“Bayan wata da watanni ina tattaunawa, na amince in shigo takara, in nemi kujerar shugaban matasa na jam’iyyarmu mai daraja, All Progressives Congress [@OfficialAPCNg].”

Kara karanta wannan

Yadda Mai Mala Buni da shugabannin APC suke fama da shari’a fiye da 200 a gaban kotu

- Rinsola Abiola

'A yau kuma?' Jama'a sun yi martani

Daga bada wannan sanarwa, wasu mutane suka dura a kan ‘yar siyasar su na tuna mata wasu kalamai da taba yi a baya a sakamkon sabani da aka samu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A 2018 ne Abiola ta yi kaca-kaca da APC, ta ce jam’iyyar ba ta tafiya da matasa, kuma ta rubuta takardar murabus. Yanzu kuma sai aka ji tana neman mukami.

‘Yar Abiola
Rinsola Abiola ta dawo APC Hoto: @RinsolaAbiola
Asali: Twitter

Kin makara: Abiola za ta fuskanci barazana

Wasu kuma su na ganin ‘diyar Marigayi MKO Abiola ta makara tun da kwanaki 15 kacal suka rage a shirya zaben a lokacin da ta bada sanarwar shiga takarar.

Irinsu Olusegun Dada wanda ya fito daga yanki daya da Abiola ya yi nisa wajen kamfe har su Hon. Abike Dabire sun amince da shi a matsayin ‘dan takararsu.

Kara karanta wannan

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

Amshi ya janye takara

Ganin cewa kujerar shugaban matasa ba za ta fito daga yankin Arewa ba, Aminu Musa wanda aka fi sani da Amshi ya janye takararsa, ya na goyon bayan Dada.

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter, AMSHI ya ce ya zabi ya mara baya ga Segun Dada a zaben, ya kuma yi kira ga magoya bayansa su bi shi.

Zan yi takara inji Sahabi Sufyan

Legit.ng Hausa ta tuntubi daya daga cikin ‘Yan Arewa maso yamma masu neman kujerar shugaban matasa na kasa, Sahabi Sufyan domin jin matsayarsa.

Malam Sufyan ya ce tun da jam’iyya ta kasa mukamai, zai hakura ya nemi mataimakin shugaban matasa na kasa, ya bada gudumuwarsa domin taimakon APC.

Burin takara

Tun a farkon 2018 ne aka ji Rinsola Abiola a wajen wani taro ta bayyanawa Duniya cewa za ta fito takarar siyasa a 2019, amma ba ta fi kujerar da za ta nema ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Wannan Baiwar Allah tayi gadon siyasa ne domin mahaifinta, Marigayi MKO Abiola ya mutu ne a kurkuku bayan yayi ikirarin lashe zaben shugaban kasa na 1993.

Ko da yake dai har yanzu ba mu san kujerar da ‘Diyar gawurtaccen ‘dan siyasar za ta nema ba, amma ta tabbatar da cewa da ita za ayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng