Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC

- Diyar marigayi MKO Abiola da ya lashe zaben shugabancin kasa na June 12, Rinsola Abiola ta fice daga jam'iyyar APC

- Abiola ta ce ta dauki matakin barin jam'iyyar ne saboda baba-kere, rashin bin tsarin demokradiyya da rashin tafiya da matasa

- A halin yanzu dai tsohuwar mamba kwamitin amintatun na APC ba ta bayyana jam'iyyar da zata koma ba

Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC
Asali: Twitter

Rinsola Abiola, diyar marigayi dan takarar shugaban kasa MKO Abiola, wadda mamba ce na kwamitin aminatatu na jam'iyyar APC ta sanar da cewa ta fice daga jam'iyyar.

A wasikar murabus dinta da New Telegarph ta gano, Rinsola ta zargi jam'iyyar da kama-karya, rashin biyaya ga ka'idojin demokradiya inda ta kara da cewa jam'iyyar bata bawa matasa daman shiga a dama da su.

DUBA WANNAN: 2019: Mataimakin Ali Modu ya ankarar da Buhari tuggun da tsohon maigidan nasa ke kulla masa

Rinsola ta ce ta bayyana shawarta na takara a karkashin inuwar jam'iyyar amma aka fada mata cewa "Ka da ta sake ta fito takarar" kuma "Ta ma dena tunanin fitowa takara," kuma muddin ba tayi biyaya ga abinda aka fada mata ba zata fuskanci hukunci.

Sai dai a halin yanzu ba ta bayyana jam'iyyar da zata koma ba.

Ga wasikar murabus dinta kamar yadda ta wallafa a shinta na Twitter @bint_moshood

Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Diyar marigayi MKO Abiola ta fice daga jam'iyyar APC
Asali: Twitter

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164