Sawun giwa: Magoya bayan Tinubu sun fadawa su Osinbajo su hakura da takara a 2023

Sawun giwa: Magoya bayan Tinubu sun fadawa su Osinbajo su hakura da takara a 2023

  • Kungiyar The Disciples of Jagaban ta nemi duk wani ‘dan takara ya janye, ya kyale Bola Tinubu
  • Shugaban The Disciples of Jagaban na kasa, Abdulhakeem Alawuje ya na neman alfarmar yarbawa
  • Alawuje yana ganin ya kamata irinsu Farfesa Yemi Osinbajo su sallamawa Tinubu a zaben 2023

Wata kungiya mai suna The Disciples of Jagaban, tayi kira ga Yemi Osinbajo da sauran ‘yan siyasan Yarbawa su ajiye burin tsayawa takarar shugaban kasa.

Punch ta ce wannan kungiya mai goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu ta bukaci mataimakin shugaban Najeriyan ya hakura da neman mulki a zabe mai zuwa.

Shugaban wannan kungiya ta DOJ, Abdulhakeem Alawuje ya fitar da jawabi a ranar Laraba, yana mai ba ‘yan siyasar yankin Kudu maso yamma wannan shawara.

Kara karanta wannan

Wajibi APC ta fita tsara a cikin jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin shugabancin APC

Abdulhakeem Alawuje ya ce dole ne duk ‘yan siyasar da suka fito daga wannan shiyya su hakura, su goyi bayan tsohon gwamnan na Legas a zaben shugaban kasa.

Jagaban ne wanda ya cancanta - DOJ

A cewar Alawuje, gwaninsu watau Bola Tinubu ne wanda ya fi dacewa ya karbi shugabancin kasar nan da zarar wa’adin Muhammadu Buhari ya zo karshe a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu
Jagaban Asiwaju Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Kungiyar Disciples of Jagaban ta na kira ga duk masu shirin tsayawa takarar shugaban kasa, su yi hakuri, su marawa takarar Tinubu baya domin ya zama shugaban kasa a 2023.”
“Tun da aka kai takara zuwa yankin Kudu maso yamma, Disciples of Jagaban ta na sake rokon duk masu hari daga Kudu maso yamma, su marawa takarar Bola Tinubu baya.”

- Abdulhakeem Alawuje

Dalilin shugaban na DOJ, Abdulhakeem Alawuje kuwa shi ne takarar Tinubu ta sha gaban ta kowa. Ko da dai har yanzu Yemi Osinbajo bai ce zai nemi takara ba.

Kara karanta wannan

Osinbajo @65: Fadar Shugaban kasa tayi magana a kan 'takarar' Osinbajo a zaben 2023

“Tinubu zai zo ne domin ya mulki ‘Yan Najeriya, ba zai yi mana mulkin ubangida da yaransa ba, zai jagorance mu ne domin mu kai ga ci.”
“Ku hakura da burinku, ku sallamawa babban ‘dan siyasa, DOJ ta na rokon jagororin APC/PDP, jagororin addini da masu sarautar gargajiya da daukacin matasan da ke tarayyar Najeriya, su mara baya ga ‘dan takarar da ya fi dacewa.”

- Abdulhakeem Alawuje

The Eagle ta ce Alawuje nemi kowa da kowa ya karbi wannan kira, ya bada gudumuwa wajen ganin shugabancin Najeriya ya fada hannun Bola Tinubu a 2023.

Yaushe za a fara kamfe?

Hukumar INEC mai cin gashin kai ta ce daga ranar 28 ga watan Satumban 2022 za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na kujerun majalisar tarayya.

INEC ta ce masu neman takarar gwamnoni a jihohi da na ‘yan majalisan dokoki za su fara fita yakin neman zabe daga Oktoban 2022 zuwa watan Maris a 2023.

Kara karanta wannan

Duk da yana Landan, Buhari ya tuna da Osinbajo yayin da ya cika shekara 65 da haihuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng