Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

  • Sabon shugaban riko na jam'iyyar APC, Abubakar Sani Bello ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya masa albarka a wannan sabon mukami nasa
  • Gwamnan na jihar Neja ya kuma bayyana hakan ne jim kasan bayan ya karbi rahoton kwamitin rabon mukamai gabannin babban taron
  • Sakataren APC ya kuma bayyana cewa Gwamna Mala Buni baya gari, cewa ya tafi ganin likita

Abuja - Sabon rikici ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya karbe ragamar mulkin jam’iyyar mai mulki gabannin babban taronta na kasa.

A wani lamari da ya zo wa mutane da dama a bazata, shine yadda Bello ya dare kujerar takwaransa na Yobe, Gwamna Mai Mala Buni, wanda ke jagorantar harkokin jam’iyyar tun bayan tsige Adam Oshiomhole, a shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja
Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja Hoto: @abusbello
Asali: Twitter

Jim kadan bayan ya karbi ragamar kula da jam’iyyar mai mulki, Bello ya karbi rahoton kwamitin rabon mukamai gabannin babban taron.

A makon da ya gabata ne aka kafa kwamitin inda aka nada gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a matsayin shugaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata hira da manema labarai bayan taron, gwamnan Neja ya ce rawar ganin da yake takawa a sakatariyar jam’iyyar na kasa na da albarkar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce zai dunga zuwa sakatariyar jam’iyyar na kasa kusan kullun don aiwatar da aikinsa.

Dalilin da yasa aka tsaurara matakan tsaro a sakatariyar APC - Gwamna Bello

Kan dalilin da yasa aka tsaurara matakan tsaro a sakatariyar jam’iyyar na kasa, Bello ya ce:

“Kun san a duk lokacin da aka ce akwai babban taro, muna tsaurara matakan tsaro.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

“A yau mun yi wani gaggarumin taro kuma dukka ciyamomi sun zo, don haka za su bi doka da oda.
“Yawancin takwarorina na a nan domin tallafa min wajen karbar rahoton. Kun san rahoton kwamitin rabon mukamai na da muhimmanci. Kuma dukka gwamnonin suna nan don taimaka mani. Yanzu, matakin shiyya, suna iya tafiya da kuma yin ayyukansu.”

A martaninsa, Sakataren APC na riko, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce Buni ya yi tafiya don ganin likita. Ba a bayyana abun da rahoton ya kunsa ba.

Na dade ina rike da mukamin shugaban APC, gwamnan Neja

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa an dan dauki tsawon lokaci yanzu da ya fara aiki a matsayin shugaban riko na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa.

Bello ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 7 ga watan Maris, bayan ya jagoranci wani taron kwamitin riko na jam’iyyar ta kasa, a sakatariyar APC da ke Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng