Gwamna ya yi magana kan shirinsa na sauya sheka zuwa APC, ya shawarci shugabannin PDP

Gwamna ya yi magana kan shirinsa na sauya sheka zuwa APC, ya shawarci shugabannin PDP

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya musanta raɗe-raɗin zai koma jam'iyyar APC nan gaba kaɗan
  • Gwamnan na jam'iyyar PDP a ranar 6 ga Maris, ya yi bayani karara cewa ba shi da shirin barin jam'iyyar dake kan turbar nasara a jihar
  • Obaseki ya shawarci wasu shugabannin PDP a jihar, waɗan da ba su son jagorancinsa su fice daga jam'iyya

Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya musanta rahoton dake yawo cewa ya fara shirye-shiryen komawa tsohuwar jam'iyyarsa APC nan gaba kaɗan.

Gwamnan ya ce bai taba tunanin ficewa daga PDP ba domin a cewarsa jam'iyyar ce ta lashe zaɓen jihar da ya gabata, kuma tana kan turban lashe kowane zaɓe a Edo.

Obaseki wanda ya yi wannan furucin a jihar ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, ya jaddada cewa ba abin da zai dakatar da PDP samun nasara a jihar Edo, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bikin sauya sheka: Dan majalisar jiha mai ci ga bar PDP, ya koma APC a Gombe

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki
Gwamna ya yi magana kan shirinsa na sauya sheka zuwa APC, ya shawarci shugabannin PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A kalamansa, gwamnan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zan fice daga PDP ba, ba zan sauya sheka ba, kowane lokaci mu zamu samu nasara a zaɓe.
"PDP ce ta sami nasara a zaben da ya gabata, kuma ita zata cigaba da nasara a kowane zaɓen jihar Edo da ƙasa baki ɗaya. Ba abin da zai dakatar da jam'iyyar mu."

Duk wanda ba zai bi ni ba ya fice - Obaseki

Bugu da ƙari, gwamnan ya bayyana cewa PDP reshen Edo a dunkule take, kuma haɗin kan ta ya nuna a naɗe-naɗe tun daga matakin gunduma.

Ya kuma shawarci waɗan da ba su kaunar jagorancin jam'iyya, su gaggauta yin murabus idan ba su son ya jagorance su.

Guardian ta rahoto Ya ce:

"Ba bu rabuwar kai a PDP-Edo, jam'iyyar mu a bude take ga mai son shigo wa. Na ji Chief Dan Orbih na yawo yana cewa ba bu jituwa a PDP, wannan cin mutuncin mambobin jam'iyya ne domin kan su a haɗe yake."

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

"Ga shi mun tattaru a nan sabida jadawalin zaɓe ya fito, haka kaɗai ya nuna muna da jituwa a tsakanin mu, mun yi naɗe-naɗe dan haka a shirye muke mu ci kowane zaɓe."

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262