PDP ta kama hanyar daidaicewa, ‘Dan cikin tsohon Gwamna yana harin kujerar Gwamna
- Ana rade-radin cewa yaron tsohon gwamnan jigawa Sule Lamido yana neman takara a zaben 2023
- Burin ‘dan tsohon gwamnan ya kawo sabani tsakanin wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Jigawa
- Wadanda suka rike mukamai a Gwamnatin Sule su na kira ga Mustafa Sule Lamido ya fito takara
Jigawa - Wani rahoto da ya fito dazu daga Daily Trust ya nuna cewa abubuwa ba su tafiya daidai a jam’iyyar PDP na reshen jihar Jigawa a halin yanzu.
Ana samun baraka a jam’iyyar adawar a dalilin rikicin takarar gwamna a zaben 2023, inda ‘dan cikin tsohon gwamna Sule Lamido ya ke neman mulki.
Tun lokacin da Alhaji Sule Lamido ya tsaida Aminu Ibrahim Ringim a matsayin ‘dan takarar gwamnan Jigawa a 2015, PDP ta fara samun matsaloli.
Wasu su na ganin Gwamna Sule Lamido ya tura Ringim ne saboda PDP ta sha kashi a hannun APC domin ‘dan da ya haifa ya samu damar mulki a 2023.
Mustapha Sule Lamido ya yi takarar kujerar Jigawa ta tsakiya a zaben 2019 a karkashin PDP, ya sha kashi a hannun Sanata Sabo Muhammad Nakudu.
Ana shari'a a kotu
Tun bayan lokacin har yau, PDP tana fama da rigingimun cikin gida, abin ya kai bangaren Aminu Ringim sun je kotu a kan zaben shugabannin jam'iyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babban kotun jihar Jigawa ba ta ba ‘yan tawaren gaskiya a karar ba. Hakan ta sa suka daukaka kara a Kano, amma ba a dace ba, yanzu ana kotun koli.
Mustafa Lamido v Hon. Jumbo
Jam’iyyar PDP ta bar hannun bangaren Ringim wanda ya yi takara a 2015, za a gwabza tsakanin Mustafa Sule Lamido da irinsu Hon. Bashir Adamu Jumbo.
Hon. Bashir Adamu Jumbo ya wakilci Kazaure/Gwiwa/Yankwashi/Roni a majalisar wakilan tarayya na tsawon shekaru 16 daga 1999 har zuwa 2015.
‘Sai Santuraki 2023’?
Wasu sun fara yi wa ‘dan tsohon gwamnan yakin ‘Santuraki for 2023’. Cikin masu zugo Mustafa akwai wadanda suka yi mulki a gwamnatin mahaifinsa.
Rahoton ya ce Nasiru Laraba wanda yake tare da tsagin Ringim ya yi tir da wannan kira, ya ce yaron tsohon gwamnan ba zai kai labari a zaben 2023 ba.
Abubakar Suleiman Kudai da Atiku Umar Katanga wadanda su na cikin magoya bayan Sule Lamido su na ganin Mustapha bai dace ya rike Gwamna ba.
Diri ya jinjinawa Buhari
Dazu aka ji cewa Gwamna Douye Diri ya ce Shugaban kasa ya nuna yana son damukaradiyya ta dore a Najeriya tun da ya sa hannu a kudirin gyaran zabe.
Sanata Douye Diri ya ce sabuwar dokar zaben da Muhammadu Buhari ya kawo za ta sa a ga karshen masu murdiya da magudi da satar akwatin zabe.
Asali: Legit.ng