Bayan ya hada mahaifiyarsa da EFCC, Abdulaziz Ganduje ya na shirin kai mahaifinsa kotu

Bayan ya hada mahaifiyarsa da EFCC, Abdulaziz Ganduje ya na shirin kai mahaifinsa kotu

  • Akwai yiwuwar Abdulazeez Ganduje ya yi shari’a a kotu da Gwamnatin mahaifinsa a jihar Kano
  • Abdulazeez Ganduje ya na kukan cewa ya yi wata kwangila, amma an ki biyansa cikon kudinsa
  • Ana zargin an ki biyan kamfaninsa kudin aiki ne a dalilin hada Hafsah Ganduje da ya yi da EFCC

Kano - Babban yaron gwamnan jihar Kano, Abdulazeez Ganduje, yana barazanar yin shari’a da mahaifinsa, Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Abdulazeez Ganduje yana yunkurin kai kara a kotu ne saboda gwamnatin mahaifinsa ta ki biyansa kudin kwangila.

Rahoton ya ce kamfanin Global Firm Nigeria Limited ya yi wa gwamnatin Kano aiki, amma Ganduje bai biya sa ragowar kudin aikinsa har N82m ba.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

A cewar jaridar, a 2020 aka ba wannan kamfani na yaron gwamnan kwangilar maida cibiyar kula da ‘yan shaye-shaye ta Mariri ta zama makarantar IDP.

50% na kudi sun fito

An bada kwangilar ne a kan kudi N189,913,590.54. A watan Mayun 2021 sai aka biya shi N94,556,795.27 a matsayin kashi 50% na yin wannan aiki.

An bar maganar da cewa ma’aikatar kananan hukumomi za ta biya kamfanin ragowar kudin 50%.

Abdulaziz da Ganduje
Abdulazeez Ganduje da Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: @daboFMOnline
Asali: Facebook

Daga baya ma’aikatar jihar ta rage kwangilar ta koma N177,619,259.36. Sai aka bukaci a kawo komfutoci da sauran kayan aiki na cikon kudin, N12,294,331.23.

Ragowar kudi sun makale

Sai bayan an kammala wannan aiki, gwamna ya ki sa hannu a biya Abdulazeez Ganduje kudin aikin da ya yi, hakan ya na nufin N82,662,464.04 sun makale.

Kara karanta wannan

Fashola: Gwamnati za ta karasa manyan ayyukan da ta tattago kafin Buhari ya sauka

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa babu mamaki Mai girma gwamnan ya ki amincewa a biya wadannan kudi ne saboda sabanin yaron na sa da mai dakinsa.

Lauyoyi sun aiko takarda

Lauyoyin Abdulazeez Ganduje sun aikawa ma’aikatar ilmi takarda su na neman a biya cikon kudin kwangilar ko su dauki matakin shari’a nan da mako daya.

Shi dai Abdulazeez Ganduje ya ce an ki biyan shi N83m da ya ke bin gwamnatin Kano ne saboda ya ki bada cin hancin kudi ga gidauniyar Ganduje Foundation.

An taso majalisa a gaba

An ji cewa kwaskwarimar da za ayi wa tsarin mulkin Najeriya zai sa shugabannin majalisar wakilai da na dattawa su rika tashi da fansho a kowace shekara.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokawa a kan biliyoyin da ake kashewa wajen biyan tsofaffin shugaban kasa da mataimakansu kudin fansho a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta gano gonakin tabar wiwi masu girman hekta 255, ta kone su kurmus

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng